Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga zaman majalisar zartaswa da ministocinsa
Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartaswa ta yanar gizo karo na 14 a fadar shugaban kasa dake Aso Villa, birnin tarayya Abuja.
An kaddamar da zaman ne misalin karfe 10 na safe inda Buhari ya bukaci aduu'ar Musulmi da Kirista.
Tare da shi a farfajiyar Council Chambers sune mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya, Boos Mustapha; mai bada shawara kan lamuran tsaro, Babagana Munguno; da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.
Hakazalika akwai Ministoci takwas dake tare da shi a wajen yayinda sauran suka shiga ta yanar gizo.
Ministocin dake wajen sune Rotimi Amaechi (Sufuri); Senator Hadi Sirika (Sufurin jirgin sama); Dr Osagie Ehanire(Kiwon Lafiya); Mrs. Zainab Ahmed(Kudi da kasafin kudi); Abubakar Malami(Antoni Janar); Babatunde Fasola(Ayyuka da jirage); Lai Mohammed(Labarai da al'adu) and Dr Isa Ali Pantami(Sadarwa da tattalin arzikin zamani).
Saurari cikakken labaran...

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Asali: Legit.ng