An kama Malamin Islamiyya da wani sun yiwa karamar yarinya fyade

An kama Malamin Islamiyya da wani sun yiwa karamar yarinya fyade

- Malamin Islamiyya ya shiga hannun 'yan sanda sakamakon yiwa wata yarinya fyade

- An kama shi tare da wani mutum da shima ya yiwa yarinyar fyade

- Yarinyar ta kaiwa Malamin karar mutumin da ya fara yi mata fyaden ne sai malamin yayi amfani da wannan damar wajen biyan bukatarshi

Wani Malamin Islamiyya mai suna, Isma'ila Saheed, mai shekaru 38 ya shiga hannu tare da wani mai suna Toliha Sabith, mai shekaru 20, sakamakon kama su da jami'an rundunar' yan sandan jihar Ogun suka yi da laifin yiwa yarinya 'yar shekara 15 fyade.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya fitar, ya ce an kama masu laifin ne a cikin karshen makon nan, bayan wacce aka yiwa fyaden ta kai karar cewa sun yi mata fyade a ranar 23 ga watan Agusta.

An kama Malamin Islamiyya da wani sun yiwa karamar yarinya fyade

An kama Malamin Islamiyya da wani sun yiwa karamar yarinya fyade
Source: Facebook

A yadda rahotannin suka bayyana, yarinyar tace Sabith ne ya fara yi mata fyade a Imedu-nla dake Mowe, sai taje ta kai karar mutumin wajen Malaminta na Islamiyya, shi ma sai yayi amfani da wannan damar ya biya bukatar shi, ta hanyar ce mata zai taimaka mata ya cire mata cikin da mutumin farkon yayi mata.

"Ta ce Sabith ne ya fara yi mata fyade, sai taje ta sanar da Malaminta na Islamiyya. Bayan yaji bayaninta, Malamin sai yace mata akwai yiwuwar ta dauki ciki sakamakon abinda wancan yayi mata, saboda haka yace zai taimaka mata ya cire mata cikin.

KU KARANTA: Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya

"Sai dai abin mamaki, maimakon ya cire mata cikin, sai yayi amfani da wannan dama yayi lalata da ita, ta hanyar sanya wani abu a gabanta, wanda ya jawo ta samu ciwo a gabanta," cewar sanarwar.

A cewar sanarwar DPO din ofishin 'yan sandan yankin, Bala Uakubu, ya sanya aje a nemo masu laifin a ranar Juma'a 28 ga watan Agusta.

Oyeyemi ya kara da cewa duka su biyun sun amsa laifinsu, kuma za a kai su bangaren yaki da safarar mutane da sanya yara aiki dake jihar domin cigaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel