Da zafinsa: Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan Edo hari, ya sha dakyar

Da zafinsa: Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan Edo hari, ya sha dakyar

- Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki hari a kan hanyar Benin-Auchi

- Sai dai jami'an tsaron da ke tare da gwamnan sun dakile wani harin, inda suka raka 'yan fashin har cikin daji

- Gwamnan na kan hanyar sa ne ta zuwa karamar hukumar Uhunmwode a jihar don gudanar da yakin zabe, lokacin da aka kai harin

Jami'an tsaron da ke tare da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki a ranar Litinin sun dakile wani hari da 'yan fashi suka kaiwa tawagar gwamnan a kan hanyar Benin-Auchi.

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar gwamnan na kan hanyar zuwa karamar hukumar Uhunmwode a jihar don gudanar da yakin zabe, lokacin da aka kai harin.

Haka zalika, rahotannin sun nuna cewa an kai masa harin ne a kauyen Erua, kusa da shelkwatar cocin Jehovah's Vitness, lamarin da ya ja tawagar ta tsaya tsak.!

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar gwamnan na tafiya a hankali ba tare da jiniya ba, lokacin da 'yan fashin suka farmake shi, da tunanin cewa wani dan siyasar ne daban.

KARANTA WANNAN: Kyauta kasar China za ta gina jami'ar sufuri da za ta ci $50m a Daura - Minista

Da zafinsa: Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan Edo hari, ya sha dakyar

Da zafinsa: Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan Edo hari, ya sha dakyar
Source: Depositphotos

Sun fara jefa bishiya a saman titin don hana motocin wucewa, tsarin da suka saba amfani da shi idan za su yiwa jama'a fashi da makami.

Majiyoyi daban daban sun bayyana cewa 'yan fashin da suka tare hanyar, ganin tawagar, suka bude wuta domin razana su, sai dai jami'an tsaron da ke tare da gwamnan suka bude masu wuta, har sai da 'yan fashin suka arce daji.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya tilasta tawagar tsayawa waje daya, na tsawon mintuna goma, kafin daga bisani suka wuce zuwa gundumar Duke (Enigie) da ke yankin.

Wata majiya a cikin jami'an tsaron tawagar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya sanar da cewa 'yan fashin sun dauka wani babban mutum ne kawai, saboda gwamnan na tafiya ba jiniya.

"Amma mun yi nasarar dakile harin na su, mun korasu har cikin daji."

Duk wani yunkuri na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Chidi Nwanbuzor ya ci turo, an gaza samunsa a wayar salula.

Daily Trust ta ruwaito cewa dai dai inda aka kaiwa gwamnan hari, wata babbar mahada ce da 'yan fashi ke cin karen su ba babbaka a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel