Tirkashi: An kashe wani mutumi da ya zargi makwabcinsa da yin lalata da matar wani

Tirkashi: An kashe wani mutumi da ya zargi makwabcinsa da yin lalata da matar wani

Wani mutumi mai suna Adekunle Adeyemi, ya fara wasan buya da jami'an tsaro bayan ya kashe makwabcinsa, Stanley Dickson, a kusa da makarantar Grammar dake Ikorodu, jihar Legas

Jaridar Punch ta gano cewa Stanley yana zargin Adekunle da kwanciya da matar wani mutumi wanda yake shima makwabcin su ne mai suna Arinze Onuoha, wanda ya tinkare shi da wannan zargi.

Tirkashi: An kashe wani mutumi da ya zargi makwabcinsa da yin lalata da matar wani

Tirkashi: An kashe wani mutumi da ya zargi makwabcinsa da yin lalata da matar wani
Source: Facebook

An gano cewa musu ya rincabe tsakanin Adekunle da Arinze, amma Stanley, wanda ya sanar da Arinze cewa Adekunle na kwanciya da matarsa baya gida.

Adekunle ya ce sai ya tinkari Stanley akan wannan sharri da yayi masa da zarar ya dawo daga wajen aiki da yamma.

Wata dake zaune a yankin mai suna Ibidunni Adegoke, ta ce lokacin da ta ziyarci yankin a ranar Lahadi, a lokacin duka Adekunle da Stanley sun dawo daga wajen aiki, rikici ya rincabe tsakaninsu, inda ta kara da cewa a lokacin da suka fara rikicin, Adekunle ya sanya wuka ya cakawa Stanley.

KU KARANTA: Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu

Haka ita ma Omotola Aderibigbe dake zaune a yankin, ta ce rikicin an fara shi a cikin dakin Stanley, inda ta ce bayan an kashe shi, Adekunle da sauran mutanen da suke tsoron kada a kama su sakamakon hannu a cikin wannan rikici sun gudu sun bar gidan baki daya.

Stanley dai direban mota ne a lokacin da yake raye, inda wakilin PUNCH ya ga motar da idon shi, inda aka ajiyeta a wajen da lamarin ya faru.

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce tuni sun mika lamarin a hannun ofishin manyan laifuka na jihar, dake Panti, Yaba, domin gabatar da kwakkwaran bincike, ya kara da cewa tuni an fara neman wanda ya aikata wannan kisa, wato Adekunle.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel