Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya

Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya

- Wani mutumi ya shiga hannun rundunar 'yan sanda bayan an kama shi da laifin yiwa wata yarinya fyade

- Mutumin ya yiwa yarinyar fyade ne a lokacin da taje wankin kayan sawa a bakin wani kududdufi

- An samu nasarar kama shi bayan yarinyar tayi ihu mutane sun jiyo ihun ta

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wani mai suna Akeem Adebayo da laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 16 fyade a bakin kogi dake Ido Osun, cikin karamar hukumar Egbedore dake cikin jihar.

A yadda wasu majiyoyi suka bayyana, lamarin ya faru da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Asabar, a lokacin da yarinyar take wanke kayanta a bakin kogin kusa da gidan mahaifinta.

Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya

Wani mutumi ya yiwa karamar yarinya fyade a lokacin da taje kogi wankin kaya
Source: UGC

An ruwaito cewa yarinyar daliba ce a makarantar sakandare dake garin, an kuma bayyana cewa mutumin da yayi mata fyaden ya buga mata karfe mai kaifi a kanta kafin yayi mata fyaden, inda ya barta cikin jini.

Yarinyar tayi ihu a lokacin da lamarin ya faru, mutanen yankin suka jiyo, inda suka garzaya wajen don ganin abinda ke faruwa, a lokacin ne suka kama mai laifin a yayin da yake shirin guduwa daga wajen.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kama mai laifin ga jaridar Punch a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki

Haka kuma LEGIT ta kawo muku rahoton yadda aka kama mutanen da suka yiwa Vera Uwaila fyade kuma suka kasheta a cikin coci.

Dalibar mai shekaru 20 da ta saba zuwa cocin tayi karatu a kowacce rana, sun kai mata hari, suka yi mata fyade sannan suka kasheta a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2020.

Bayan shafe watanni ana bincike, rundunar 'yan sandan jihar ta kama masu laifin masu suna Nelson Ogbebor, Akato Valentine, Mrs Tina Samuel, Mrs Mary Ade, Nosa Osabohien da kuma Collins Ulegbe.

An gano masu laifin ne bayan 'yan sandan sun bi diddigin wayar marigayiyar, inda aka sameta a hannun daya daga cikin masu laifin, Nosa Osabohien.

Nosa wanda yake aikin gyaran waya ya ce ya sayi wayar ne a hannun wadanda suka kashe vera, Collins Uyegbulen. Ya kai 'yan sandan inda Collins yake, inda shi kuma ya bayyana cewa yana da hannu a kisan. Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel