Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna)

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna)

Mazauna wasu kauyukan da ke iyaka a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, wadanda 'yan bindiga suka hargitsa cikin kwanakin nan, sun bayyana mummunan halin da suka shiga.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Augustan 2020, mazauna kauyukan Tsambaye, Zango Mai Rumbuna da Karauki, maza, mata da kananan yara duk sun bar gidajensu, gonaki da sauran kadarorinsu don samun mafaka.

Sun yada zango a wata makarantar firamare da ke tsakiyar garin Jibia don gujewa ci gaban cin zarafi, kashe-kashe da fyade da 'yan bindiga ke musu.

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna)

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

A yayin da jaridar Daily Trust ta ziyarci sansanin, wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun bayyana yadda 'yan bindigar ke kai musu hari a kuayukansu tare da yi wa mata fyade. Suna kashe wadanda suka nemi hana su cimma manufarsu tare da yin awon gaba da kadarorinsu.

Daya daga cikin matan da aka yi wa fyade ta bada labarin yadda aka yi wa wani namiji yankan rago kuma aka yi awon gaba da mata biyu a gabanta. Daya daga cikinsu kuwa mai jego ce aka sace da jinjirin.

"Wannan shine karo na uku da ake yi wa namiji yankan rago a kauyenmu. A gabana suka tafi da mata biyu. Daya daga cikinsu bata dade da haihuwa ba. Ko zanin goyon jaririn basu barta ta dauka ba. Allah kadai ya san halin da suke ciki," tace.

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna)

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Wata dattijuwar mata mai suna Malama Hannatu, ta ce, "Kattin maza biyar suka fado min daki a ranar da suka kutso kauyenmu. Sun sameni da siket kadai. Sun tsorata ni tare da umartar in fito musu da kudade. Duk da na ce bani da shi, sun ce karya nake.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun halaka kansilan PDP mai ci

"Sun kwashe fiye da sa'a daya suna duba dakina amma basu samu komai ba. A haka dai suka gaji suka kara gaba. Tun daga wannan lokacin, rana tana faduwa nake shiga halin fargaba da tashin hankali. Hakan ne yasa na bar garin."

Wata matashiyar budurwa mai suna Rabi, ta sanar da yadda 'yan bindigar suka kashe maza takwas a kauyensu yayin da 'yan bindigar suka shiga, har da dagaci.

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna)

Fyade, fashi da makami da hargitsi: 'Yan gudun hijira a Katsina sun koka (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

"Bari in fada muku gaskiya, kusan dukkan mata masu matsakaicin shekaru sai da aka yi musu fyade a wannan ranar.

"Sun yi wa mazan duka, hatta kananan yara basu bari ba. A haka suka kwashe mana kayan abinci suka yi awon gaba da shi. Abubuwan da suka kasa dauka, sun yi musu kashi sannan suka yi gaba," Rabi ta labarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel