Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade

Wasu samarin kasar Afrika ta Kudu sun bayyana yadda manyan mata ke yi musu fyade a lokacin da suke da kuruciyarsu, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna @TyrenndumisoB ya fara bada labarin yadda aka yi masa fyade yana da shekaru 14 a duniya.

Matashin ya bayyana cewa ya fara saduwa da mace a lokacin da yake da shekaru 14 kacal a duniya kuma yana mataki na 7 a makaranta.

"Smangele Kunene Zulu ce ta yi min fyade. Abun takaicin shine yadda ta cire kwaroron robar bayan da muka kammala kashi na farko. Bata yi min da wasa ba kuma a kazance ta yi min komai," yace.

Jama'a da dama a kafar sada zumuntar zamanin, ballantana samari, sun fito inda suka dinga jimami tare da bayanin yadda makamancin hakan ta faru da su.

Saurayin ya cigaba da cewa, "Wasu daga cikinmu za su tausaya min, amma wasu dariya abun zai basu. Hatta 'yam mata idan suka ji labarina, su kan yi min dariya. Daga nan na tsani jima'i kwata-kwata."

Babu jimawa da wannan wallafar, samari suka dinga bayanin abinda ya faru da su a hannun manyan mata.

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu

Sauran matasan kasar Afrika ta kudun sun bayyana labaransu masu cike da alhini a kan yadda manyan matan suka yi amfani da damarsu wurin lalata su. Hakan ne yasa aka gane cewa lamarin ya zama ruwan.

Wani matashin ya sake bayanin abinda ya faru da shi inda yace, "ban san ko zan iya sanar da mahaifiyata ba, amma ina tunanin yanzu na yi latti. Mai aikinmu ce ta lalata ni tun ina karami."

Zakhele kuwa cewa yayi, "Ina da shekaru bakwai kanwar mahaifiyata ta ke dukana, ta hana ni abinci tare da yin lalata da ni. Ta shafa min cutar sanyi. Akwai lokacin da har gida na bari. Dogon labari ne kuma ban taba sanar da mahaifiyata."

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

Wani matashi mai suna mthokozisi maphumulo kuwa cewa yayi, "ina tuna lokacin da nake da shekaru 16 zuwa 17 a duniya. Na je gidan wata kawata amma sai na yi rashin sa'ar tarar da ita. Mahaifiyarta na samu inda ta bani ruwan lemo.

"Kafin in san me ke faruwa, sai ganinmu nayi muna lalata. Daga nan kuwa muka ci gaba. A halin yanzu shekaru na 27 kuma muna tare.

"Babbar ma'aikaciya ce a fannin lafiya. Tana biya min kudin makaranta kuma a halin yanzu na kammala karatu. A duk lokacin da nayi yunkurin barinta, tana min muguwar barazana."

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade

Labarin samari: Yadda manyan mata suke yi mana fyade. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel