Yadda ‘yan iska suka yi wa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a Ibadan

Yadda ‘yan iska suka yi wa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a Ibadan

Rahotanni sun kawo cewa wasu ‘yan iska sun yiwa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a karamar hukumar Akinyele da ke jihar Oyo.

Ana ta samun lamuran kashe-kashe don asiri a yankin, wanda yake a Ibadan tun a watan Yuni kuma babban wanda ake zargi da aikata wasu daga cikin kashe-kashen shine Sunday Shodipe.

Yana a hannun ‘yan sanda a tsare biyo bayan kama shi sannan ya tona cewa shi ya aika wasu kisan da aka yi a yankin.

Amma wannan matashiya da aka kashe mai shekaru 18, Mary Daramola, an tattaro cewa an yi mata fyade ne har lahira a garin Alabata, yayinda wasu suka ce wani mutum mai suna Toheed Ganiyu ne ya yi mata fyade ne sannan ya kashe ta.

Yadda ‘yan iska suka yi wa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a Ibadan

Yadda ‘yan iska suka yi wa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a Ibadan Hoto: Premium Times
Source: Depositphotos

An tattaro cewa an kama wanda ya aikata laifin yayinda yake kokarin jefar da gawarta a wani daji da ke garin.

Yayinda aka kama babban wanda ake zargi, an tattaro cewa sauran wadanda ke taya shi jefar da gawar sun tsere kuma cewa ‘yan sanda na nan suna bin sahunsu.

Marikiyar matashiyar da aka kashe, Misis Folakemi Adedeji, ta nuna bakin ciki kan lamarin, ta yi kira ga ‘yan sanda da su gudanar da bincike a tsanaki domin gaskiya ta yi halinta kan lamarin.

Baale na Alabata, Cif Rasaq Ajimoti, wanda ya koka kan lamarin fyaden da kashe- kashe a yankin, ya roki matasan yankin da su kwantar da hankalinsu. Ya ce ‘yan sanda na kan lamarin, inda ya kara da ewar yana da tabbacin za a yi adalci.

Cif Rasaq wanda ya nuna bakin ciki kan lamarin, ya ce mazajen da suka aikata ta’asar sun yi kokarin jefar da gawar a daji lokacin da wani ya gansu sannan ya nemi doki.

KU KARANTA KUMA: Allahu akbar: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da lamarin a wayar tarho, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce: “An ce wani Taoheeb Ganiyu na garin Alabata Moniya ya kama matashiyar mai shekaru 18, Mary Daramola zuwa dakinsa sannan ya shayar da ita giya kafin ya yi lalata da ita.

“An ga Mary a mace da maniyyi a matancinta da jini a bakinta. An kama wanda ake zargin kuma an gudanar da binciken farko a ofishin ‘yan sandan Moniya. Daga bisani an tura lamarin ga sashin binciken manyan laifi, Iyaganku.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel