Da duminsa: Jihar Flato na kan gaba yayinda Korona ta harbinsabbin mutane 250 a Najeriya

Da duminsa: Jihar Flato na kan gaba yayinda Korona ta harbinsabbin mutane 250 a Najeriya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 250 a fadin Najeriya.

Kwana hudu a jere yanzu jihar Plateau na zarce Legas da Abuja wajen yawan adadin sabbon wadanda suka kamu da cutar.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Asabar 29 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 250 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-69

FCT-41

Lagos-21

Delta-14

Kaduna-14

Bayelsa-13

Enugu-13

Ekiti-11

Bauchi-9

Ogun-8

Edo-7

Oyo-7

Rivers-6

Adamawa-4

Osun-4

Nasarawa-3

Ebonyi-2

Kwara-2

Gombe-1

Imo-1

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel