Gwamnan Legas ya bada umurnin bude jami'o'i da makarantun jihar

Gwamnan Legas ya bada umurnin bude jami'o'i da makarantun jihar

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin bude dukkan jami'o'i mallakan gwamnatin jihar daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai yau Asabar, kamar yadda TheCable ta shaida.

Hakazalika ya bayyana cewa da yiwuwan za'a bude makarantun sakandaren jihar fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020.

An rufe makarantun ne a watan Maris sakamakon bullar cutar Korona.

Jihar Legas ke kan gaba wajen yawan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya.

"Wannan sanarwar da mu kayi ba yankakkiya bace, kuma zamu iya canzawa dubi ga irin yadda abubuwa suka gudana da kuma sharrudan kare kai daga ma'aikatar kiwon lafiya." Sanwo-Olu yace.

A yanzu, daliban ajujuwan karshe masu zana jarabawar fita daga makarantan sakandare kadai ke zuwa makaranta.

Gwamnan Legas ya bada umurnin bude jami'o'i da makarantun jihar
Gwamnan Legas ya bada umurnin bude jami'o'i da makarantun jihar
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng