Yan bindiga sun sace dan sanda, jami'in NSCDC tare da wasu mutum jihar Kaduna

Yan bindiga sun sace dan sanda, jami'in NSCDC tare da wasu mutum jihar Kaduna

Wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne sun yi awon gaba da jami'in dan sanda, jami'in hukumar Sibil Defens NSCDC, wata yarinya da wani mutum a jihar Kaduna.

An dauke jami'an tsaron biyu ne a gidajensu dake unguwar Maraban Rido, karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a daren Alhamis, 27 ga Agusta, 2020.

Yan bindigan sun kai hari unguwar ne cikin dare misalin karfe 12 inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin suka yi awon gaba da su.

Duk da cewa hukumar yan sanda bata tabbatar da dauke jami'inta ba har yanzu, kakakin hukumar NSCDC na jihar Kaduna, Orndiir Terzungwe, ya tabbatarwa Channels TV labarin.

Ya ce an yi awon gaba da jami'insu ne a gidansa kuma an kaishi wani wuri.

Terzungwe ya ce hukumar ta kaddamar da farautar yan bindigan domin ceton jami'insu da kuma damkesu.

Yan bindiga sun sace dan sanda, jami'in NSCDC tare da wasu mutum jihar Kaduna
Yan bindiga sun sace dan sanda, jami'in NSCDC tare da wasu mutum jihar Kaduna
Source: UGC

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel