Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan karuwancin da yan sansanin gudun Hijra ke yi

Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan karuwancin da yan sansanin gudun Hijra ke yi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan yadda karuwanci da ayyukan assha ke yawaita a cikin sansanin yan gudun hijra dake jihar Borno.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda wata tawagar kwamitin majalisar dattawa kan harkoki na musamman ta ziyarcesa karkashin jagorancin, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, a Maiduguri, LEADERSHIP ta ruwaito.

A ranar Juma'a, rahoto ya bayyana cewa kwamitin majalisar da ta kunshi Sanatoci 12 sun tafi Borno domin duba ayyuka da nasarorin da hukumar cigaban Arewa maso gabas NEDC ta samu a Borno da sauran jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan karuwancin da yan sansanin gudun Hijra ke yi

Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan karuwancin da yan sansanin gudun Hijra ke yi
Source: UGC

Saurarin cikakken bayani...

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel