Da dumi: Yan sanda sun hallaka dan babur kan cin hancin N50

Da dumi: Yan sanda sun hallaka dan babur kan cin hancin N50

Wasu jami'an yan sanda a jihar Oyo ranar Laraba sun yiwa wani dan achaba masi suna Biola duka har lahira a unguwar Born Photo dake garin Ibadan, babbar birnin jihar.

Bayanan da Sahara Reporters ta shimfido ya nuna cewa an kashe Biola ne yayinda yake hanyar zuwa asibiti daukan matarsa saboda ya ki baiwa yan sandan na goron naira hamsin kacal.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Segun, ya bayyana cewa yana hanyarsa ta dawowa daga aiki lokacin da abin ya faru.

Ya ce abin ya zama ruwan dare yadda yan sanda ke cin zarafin direbobin motocin haya da yan babur da aka fi sani da Okada.

"Yan sandan sun tsayar da marigayin kuma suna kokarin amsan kudi daga hannunsa amma ya ki basu saboda yana kokarin zuwa asibiti daukan matarsa."

"Yan sandan suka dage cewa sai ya basu kudin kuma suka daina sauraron abinda yake fada."

"Kawai sai daya daga cikinsu ya bugeshi da bindigansa. Bayann haka sauran suka sa hannu suka cigaba da dukansa har sai da numfashinsa ya dauke," Mai dion shaidan ya laburta.

Da dumi: Yan sanda sun hallaka dan babur kan cin hancin N50

Da dumi: Yan sanda sun hallaka dan babur kan cin hancin N50
Source: Twitter

A wani labaran daban, Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta amince da fitar da N10bn a matsayin tallafi ga direbobi da kungiyoyin da ke kula da su.

A cewar ministar zirga zirga na cikin gida, Sanata Gbemisola Saraki, tallafin zai taimaka wajen rage wahalhalun da direbobin ke fuskanta a dalilin annobar COVID-19.

Ta yi nuni da cewa yanzu haka kudaden na a hannun ma'aikatar masana'antu da kasuwanci, tana mai cewa ma'aikatar ta na kan shirye shiryen rabon kudaden.

Ministar ta bayyana hakan ne a ziyarar da shugaban kungiyar direbobi ta kasa (PTONA), Engr. Isaac Uhunwagbo ya kai mata tare da kwamitin amintattu na kungiyar a Abuja.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan watsa labaran ministar, Eric Ojiekwe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel