Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

- 'Yan sanda sun samu nasarar kama mutane shida da suke da hannu a kisan, dalibar jami'ar Benin Vera Uwaila

- An samu nasarar kamasu ne bayan shafe watanni ana gabatar da bincike, inda a karshe aka gano wayarta a hannun wani

- Masu laifin sun bayyana cewa wata mata ce ta basu naira miliyan daya tace su yiwa budurwar fyade su kasheta sannan su gogo mata jinin gabanta a jikin tsumma

Rundunar 'yan sandan jihar Edo sun kama mutane shida da suke da hannu a kisa da fyade da aka yiwa Vera Uwaila, dalibar aji daya a jami'ar Benin, wacce suka kashe a cikin Coci.

Dalibar mai shekaru 20 da ta saba zuwa cocin tayi karatu a kowacce rana, sun kai mata hari, suka yi mata fyade sannan suka kasheta a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2020.

Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila
Source: Facebook

Bayan shafe watanni ana bincike, rundunar 'yan sandan jihar ta kama masu laifin masu suna Nelson Ogbebor, Akato Valentine, Mrs Tina Samuel, Mrs Mary Ade, Nosa Osabohien da kuma Collins Ulegbe.

An gano masu laifin ne bayan 'yan sandan sun bi diddigin wayar marigayiyar, inda aka sameta a hannun daya daga cikin masu laifin, Nosa Osabohien.

Nosa wanda yake aikin gyaran waya ya ce ya sayi wayar ne a hannun wadanda suka kashe vera, Collins Uyegbulen. Ya kai 'yan sandan inda Collins yake, inda shi kuma ya bayyana cewa yana da hannu a kisan.

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki

Collins yace shine ya bugawa Vera wani abu a kai, yayin da sauran kuma suka fara yi mata fyade. Ya bayar da sunan sauran 'yan kungiyarsu da suka hada da Akato Valentine da Collins Ogbebor.

Ya bayyanawa 'yan sanda cewa wata mata ce mai suna Mary Ade ta basu naira miliyan daya tace su kasheta, sannan ta basu tsumma tace su gogo mata jinin gabanta.

Haka wata mata da ita ma keda hannu a kisan, an kamata a yayin da take hana 'yan sanda kama danta, Lucky wanda yake daga cikin masu laifin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Johnson Kokumo, wanda ya gabatar da masu laifin, ya ce binciken da aka gabatar akan Uwaila an gano cewa anyi mata fyade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel