Halima Abubakar: A yanke mazakutar wanda aka kama da laifin fyade

Halima Abubakar: A yanke mazakutar wanda aka kama da laifin fyade

- Jarumar fim Halima Abubakar ta bayar da shawarar yi wa dukkanin masu fyade dandanka

- Halima Abubakar ta koka kan cewa lamarin fyade na sake kamari duk da kokarin da ake yin a ganin an yakice shi

- Ta bayyana masu aikata fyade a matsayin babban hatsari

Shahararriyar jarumar wasar kudu, Halima Abubakar ta bayar da shawarar cewa a yi wa dukkanin masu fyade dandanka.

Jarumar wacce ke da haihuwar ‘da daya ta ce lamarin fyade na sake kamari duk da kokarin da ake yi na ganin an yakice shi.

Ta kara da cewar “dabara ya rage garemu domin kare al’ummanmu ta hanyar kare yaran sauran mutane ba wai muyi kunnen uwar shegu ba idan lamarin ya shafi wasu daban ba wani namu ba.”

Ta kara da cewar “masu fyade babban hatsari ne” sannan ta bayar da shawarar cewa a yanke masu mazakutansu.

Halima Abubakar: A yanke mazakutar wanda aka kama da laifin fyade

Halima Abubakar: A yanke mazakutar wanda aka kama da laifin fyade Hoto: The Whistler NG
Source: UGC

Ta wallafa a shafinta na Instagram: “Yadda muke tashi tsaye wajen yaki da fyade da rashin adalci haka kuma mummunan lamarin ke kara hauhawa.

"Ku kare muhallinku

"Ku kare ‘ya’yan sauran mutane

"Kada ku ce menene naku a ciki

"Akwai abubuwa da dama na kauna da za ku fadi

"Ku yanke mazakutar. Masu fyade hatsari ne babba"

KU KARANTA KUMA: Mijina matsafi ne, yana son ya yi kudi dani - Wata mata ta roki kotu a raba aurenta

A wani labari na daban, wani fitaccen mai fashin na'ura mai kwakwalwa da wayoyi mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas.

Ya shiga hannu ne bayan fashin da yayi wa wata mata a Ori-Okuta da ke yankin Agric da ke Ikorodu wurin karfe 11:00 na dare a ranar 29 ga watan Maris.

Kakakin rundunar 'yan sandan yanki na biyu, DSP Hausa Idris Adamu, ta ce wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade a gaban 'ya'yanta bayan kammala musu girkin abinci.

Oladiran, wanda ya tsere bayan matar ta fasa ihu, an kama shi bayan bayanan da aka samu cewa yana shakatawa a wani otal a jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel