An gurfanar da wata budurwa a gaban kotu kan tayi shigan banza da ta nuna tsiraicinta

An gurfanar da wata budurwa a gaban kotu kan tayi shigan banza da ta nuna tsiraicinta

- An gurfanar da wata budurwa a gaban kotun majistire a jihar Ribas da laifin shigar banza da tayi a cikin al'umma

- Haka kuma ana zargin budurwar da laifin daukar hoton jami'in dan sanda dake kan aiki ba tare da masaniyar shi ba

- Alkalin kotun dai ya bayar da belin ta akan kudi naira dubu dari da kuma shaidu

A ranar 25 ga watan Agusta ne, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta kama wata budurwa mai shekaru 21, mai suna Blessing Levi, inda ta gurfanar da ita a gaban kotun majistire dake Choba, cikin karamar hukumar Obio/Akpor, bisa laifin yin shiga ta tsiraici da kuma daukar hoton dan sanda dake kan aiki ba tare da sanin shi ba.

'Yan sandan sun gurfanar da Blessing a gaban kotun kan laifuka guda biyu, da suka hada da shigar banza, da kuma daukar hoton jami'in dan sandan dake kan aiki ba tare da sanin shi ba.

An gurfanar da wata fitsararriyar budurwa a gaban kotu kan tayi shiga banza da ta nuna tsiraicinta

An gurfanar da wata fitsararriyar budurwa a gaban kotu kan tayi shiga banza da ta nuna tsiraicinta
Source: Twitter

A yadda rahoton ya nuna, Blessing ta dauki hoton jami'in dan sandan a watan Mayun shekarar 2020 ba tare da sanin shi ba. Haka kuma rahoton ya kara da cewa Blessing tayi shigar banza da za ta saka duk wanda ya kalleta ya shiga wani hali, kuma hakan zai jawo matsala a tsakanin al'umma.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a lokacin da ake karantowa Blessing abubuwan da tayi, ta amsa duka laifinta.

KU KARANTA: Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda

Sai dai kuma alkalin kotun majistire din, Israel Agbaeaor, ya bayar da belinta akan kudi naira dubu dari da kuma shaidu. Alkalin ya ce wanda zai tsaya matan dole ya kasance yana da gida a wannan yankin da kotun take, sannan kuma zai bayar da hotunan shi guda biyu.

Alkalin ya umarci a cigaba da tsareta a ofishin 'yan sanda har zuwa lokacin da za a cika ka'idojin belinta.

Daga nan alkalin ya daga sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Oktobar shekarar 2020 din nan da muke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel