Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu nasaran farko a kotun koli

Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu nasaran farko a kotun koli

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu nasara a kotun kolin tarayya.

Kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar Democratic People’s Party ta shigar na kalubalantar nasarar Yahaya Bello a zaben 2019, rahoton TVC.

Bayan haka, kotun ta dage karar dake tsakanin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP da All Progressives Congress APC zuwa ranar 31 ga Agusta, 2020.

Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu nasara a kotun koli
Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu nasara a kotun koli
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel