Miji ya daure tsohuwar matarshi ya yankewa sabon saurayinta azzakari da wuka akan idonta

Miji ya daure tsohuwar matarshi ya yankewa sabon saurayinta azzakari da wuka akan idonta

Wani mutumi dan kasar Spain ya daure tsohuwar matarsa da igiya, sannan ya tilasta ta kalli lokacin da yake yankewa sabon saurayinta mazakuta da wani takobi a gidan da suka je shakatawa a kasar Portugal

Mutumin mai suna Carlos Sande Fidalgo da tsohuwar matarshi, mai suna Nuria Rodriguez Gonzalez, an ruwaito cewa sun rabu a watan Maris din shekarar 2020. Sai dai kuma yaki ya dauki kaddara ya hakura, hakan ya sanya ya kaiwa sabon saurayinta hari, inda daga baya kuma ya kashe kanshi.

Carlos ya kashe kanshi ta hanyar fadowa daga kan gada, bayan ya kashe sabon saurayin budurwar tashi mai suna, Luis Miguel Fernandez.

Miji ya daure tsohuwar matarshi ya yankewa sabon saurayinta azzakari da wuka akan idonta

Miji ya daure tsohuwar matarshi ya yankewa sabon saurayinta azzakari da wuka akan idonta
Source: Facebook

'Yan sanda sun bazama farautar Carlos bayan Nuria, ta samu ta kunce kanta daga wajen da ya daureta lokacin da yake yiwa saurayin nata kisan gilla.

Jami'an tsaron sun tsaya da binciken bayan sun gano cewa wanda ake zargin ya kashe kanshi.

Wannan lamari da ya faru a wani karamin kauye na kasar Portugal dake Gondufe, kusa da iyakar kasar ta Arewa da yankin kasar Spain, har yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin a ranar Asabar 15 ga watan Agusta.

An samu gawar Carlos, wanda yake dan kasuwa ne dake zaune a birnin Galicia dake Vigo, an same shi a ranar Laraba da safe, 19 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta

A yadda rahotanni suka nuna, 'yan sanda suna zargin cewa tsohon mijin Nuria ya sanya na'urar da take nuna masa duk inda ta shiga, hakan ya sanya yake gano duk wurin da take bayan rabuwarsu a farkon shekarar nan.

Wata majiya daga 'yan sandan ta ce Carlos ya bibiyi motar tsohuwar matarshin yaje gidan da take ya sameta da sabon saurayin nata, hakan ya sanya ya dauki wannan mataki cikin kishi.

A lokacin da yayi wannan aika-aika, Fidalgo ya daure hannun tsohuwar matarshin da igiya. Inda ya dauki kimanin awa shida yana yankar azzakarin saurayin nata akan idon ta, ta hanyar amfani da wuka da kuma takobi kirar kasar Japan mai suna Katana.

'Yan sanda sun gano halin da ake ciki bayan wanda ake zargin ya bar gidan, sannan kuma tsohuwar matarshin da ya daure ta samu ta kubuta ta sanar da 'yan sandan.

An gano cewa yayi amfani da motar Nuria ne ya gudu bayan ya kammala wannan aika-aika, inda daga baya kuma ya canja mota ya shiga motarshi mai kirar BMW 740 baka, bayan an tsinci motar a wajen gadar.

An tsinci gawarshi da misalin 10 na safiyar ranar Laraba 19 ga watan Agusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel