Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta

Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta

‘Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 40 da aka ambata da suna Gbenga Taiwo, bisa zargin lalata ‘yar cikinsa mai suna Folake.

Taiwo wanda ya kasance bazawari na zama tare da ‘yarsa mai shekaru 15 a wani gida da suke haya a Baruwa, yankin Ipaja da ke jihar Lagas.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mahaifin yarinyar na yawan cin zarafinta ta hanyar tura yatsa a matancinta tun tana ‘yar shekara 13 a duniya.

Sakamakon gajiya da cin zarafin da yake mata, sai Folake ta yi karar mahaifin nata a gaban mai gidan da suke haya inda shi kuma ya gargadi Taiwo da ya janye daga ta’asar da yake yi.

An tattaro cewa ya ci gaba da aikata hakan lamarin da ya sa yarinyar kai karansa wajen kawunta kwanaki.

Yayinda kawun nata ke kokarin magance lamarin cikin sirri, sai wani makwabci ya bangado lamarin sannan ya yi kara.

Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta

Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta Hoto: Premium Times
Source: Depositphotos

An tattaro cewa an kai karar lamarin ga offishin ‘yan sandan Ipaja sannan aka kama Taiwo a ranar Asabar da ya gabata.

Jagoran kungiyar kare hakkin yara da ke bibiyar lamarin, Mista Ebenezer Omejalile, ya fada ma City Round cewa Taiwo ya yi ikirarin cewa yana zargin Folake na bin maza don haka ya yanke shawarar binciken budurcinta da yatsarsa.

Ya ce: “Mahaifin yarinyar ya sha cin zarafinta tun tana shekara 13. Ya kai kimanin shekaru 40 a duniya kuma ya kasance mai aikin gyaran wuta da ya yi ritaya.

“Kafin kawun yarinyar ya shiga lamarin, wani Mista Alagba, yarinyar ta gaji da muguntan da mahaifinta ke yi mata sannan ta sanar da mai gidan da suke haya wanda ya tunkari mahaifin nata a kan ya daina mugun aikin da yake yi sannan ya sanar dashi illar abunda yake yi.

“Amma sai ya yi kunnen uwar shegu sannan ya ci gaba da lamarinsa hart a kai duk lokacin da yake aikin dare, sai ya tafi da yarinyar domin ya ci gaba da lalata da ita har sai ya gamsu.

“Mutumin ya yi ikirarin cewa ya ga wasu hotuna a wayar ‘yar tasa sannan yana zargin tana bin maza. Ya ce bai tara da ita ba kawai dai ya yi amfani da hannunsa ne wajen duba ko budurwace ko akasin haka.”

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun yi awon gaba da makamai

An tattaro cewa ‘yan uwan Taiwo sun yi ikirarin cewa ya yi fama da matsalar kwakwalwa a 2018 sannan aka kwantar da shi a wani asibiti mai zaman kansa, asibitin Ise Oluwa da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Wani rahoto dauke da sa hannun Shugaban likitocin asibitin, Dr Kayode Ojomo, ya nuna cewa an kwantar da Taiwo a asibitin a ranar 1 ga watan Oktoba, 2018 sakamakon korafi na kunci.

Rahoton ya kara da cewar: “A yanzu haka yana kwance an bashi gado kuma za a sallame shi da zaran an samu ci gaba.”

“Yana ta nuna wasu bakin hallaya masu ban al’ajabi a cikin kurkuku. Wasu lokutan ya kan cire kayan jikinsa,” in ji wata majiya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bala Elkana, ya tabbatar da kamun Taiwo.

Ya ce: “An fara bincike a kan lamarin kuma za a gudanar da gwaji domin tabbatar da lafiyar kwakwalwar wanda ake zargin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel