Yan bindiga sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun yi awon gaba da makamai
1 - tsawon mintuna
Wasu yan bindiga a ranar Juma'a sun kai hari ofishin yan sandan unguwar Ikolaba, Ibadan, birnin jihar Oyo.
Tabbatar da gaskiyar lamarin, kakakin hukumar yan sandan jihar Oyo, Gbenga Fadeyi, ya bayanawa Channels TV cewa ya samu labarin harin misalin karfe 9 na dare amma bai da tabbacin irin bannar da akayi.
Fadeyi ya kara da cewa an tura karin jami'ai ofishin yan sandan Ikolaba yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.
Yan bindigan sun hallaka dan sanda daya kuma da dama sun jikkata.
Bayan kashe dan sandan, sun rarike makaman da ke ofishin yan sanda.

Asali: UGC
Asali: Legit.ng