Ayo Salami: Ibrahim Magu ya na so ya san jerin zargin da ke kan wuyansa

Ayo Salami: Ibrahim Magu ya na so ya san jerin zargin da ke kan wuyansa

Tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya rubutawa kwamitin Ayo Salami takarda, ya na neman a fito masa da jerin duk zargin da ake yi masa.

Jaridar The Cable ta ce Ibrahim Magu ya rubuta takarda ga wannan kwamiti da ke binciken aikin da ya yi a hukumar EFCC tsakanin 2015 zuwa 2020 ne a cikin makon nan.

Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin da tsohon babban Alkalin babban kotun daukaka kara na kasa, Ayo Salami ya ke jagoranta ne a ranar 6 ga watan Yuli, 2020.

Hakan na zuwa ne bayan an tsare Ibrahim Magu a ofishin ‘yan sanda da ke Abuja. Magu wanda shi kan shi ‘dan sanda ne, ya shafe kwanaki tara ana yi masa tambayoyi.

A wata wasika da Magu ya rubuta a ranar 20 ga watan Agusta, ya bukaci kwamitin binciken ya bayyana masa duk laifuffukan da ake zargin ya aikata a lokacin ya na ofis.

Tsohon shugaban na EFCC ya rubuta wannan takarda ne ta hannun lauyansa, Wahab Shittu. Wannan ce wasika ta uku da ya rubutawa kwamitin a madadin Magu.

KU KARANTA: Abin da Magu ya ke so kwamitin bincike ya yi masa

Ayo Salami: Ibrahim Magu ya na so ya san jerin zargin da ke kan wuyansa

Shugaban kasa tare Ibrahim Magu
Source: Facebook

“Ku duba sashe na 36(6)(A)(B) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ce: Duk wanda ake tuhuma da laifi, ya na da hakkin a fada masa zargin da ake yi masa a harshen da zai iya fahimta.”

Lauyan ya ce wannan doka ta kuma bukaci: “A bada isasshen lokacin domin wanda ake zargi ya shirya kare kansa.”

“La’akari da wannan, mu na bukatar kwamitin bincike ya bamu wadannan abubuwa domin mu shirya kare kanmu:

“Takardun duk korafe-korafe da bayanan da aka gabatar a kan wanda mu ke karewa a gaban wannan kwamiti, da samun iznin taba duk wasu takardu da aka gabatarwa kwamitin, da duk wasu takardu masu alaka da za su yi mana amfani wajen kare wanda mu ke wakilta.”

Wahab Shittu ya roki wannan kwamiti ya yi la’akari da lokacin da ake da shi, ya bada wadannan takardu da aka bukata.”

Lauyan ya ke cewa ta haka ne za a yi wa Ibrahim Magu adalci kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel