Karti 30 sun yiwa yarinya 'yar shekara 16 fyade da karfin tsiya a wani otel bayan ta kwankwadi barasa

Karti 30 sun yiwa yarinya 'yar shekara 16 fyade da karfin tsiya a wani otel bayan ta kwankwadi barasa

Wani rahoto daga kasar Isra'ila ya nuna cewa wasu karti guda 30 sun taru sun yiwa wata karamar yarinya fyade a wani otel a lokacin da taje wajen domin ta sha barasa da kawayenta

Wasu gardawan maza guda 30 sun yiwa wata yarinya 'yar shekara 16 fyade a wajen shakatawa na Eilat dake kasar Isra'ila.

A rahoton da jaridar Times ta kasar Isra'ila ta fitar, yarinyar taje ofishin 'yan sanda a ranar Juma'ar da ta gabata 14 ga watan Agusta, inda ta bayar da rahoton yadda mazan suka yi mata fyade a lokacin da ta sha giya ta bugu a dakin otel.

Karti 30 sun yiwa yarinya 'yar shekara 16 fyade da karfin tsiya a wani otel bayan ta kwankwadi barasa

Karti 30 sun yiwa yarinya 'yar shekara 16 fyade da karfin tsiya a wani otel bayan ta kwankwadi barasa
Source: Facebook

'Yan sandan sun bayyana cewa tuni sun cafke mutane biyu daga cikin masu laifin, kuma daya daga cikin wadanda ake zargin ya bayyanawa masu binciken shi cewa maza da yawan gaske sun yi lalata da yarinyar.

Wasu daga cikin mazan an ruwaito cewa sun dauki bidiyo a wayoyinsu lokacin da suke lalata da yarinyar, a rahoton da jaridar Isra'ila ta Haaretz ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin bayan 'yan sanda sun gano bidiyon da aka nada lokacin da ake yiwa yarinyar fyaden.

'Yan sandan sun bayyana cewa yarinyar ba wai taje otel din bane don ta kwana, ta jene kawai don ta sha giya tare da kawayenta. Amma a lokacin da ta shiga bandaki, sai suka dauketa ta karfin tsiya zuwa daya daga cikin dakin otel din, inda suka yi mata fyade ba tare da kowa ya san kowa ba.

KU KARANTA: Uwa da 'ya'yanta guda biyu sun kashe kansu bayan 'yan uwansu sun dora musu karan tsana sakamakon mutuwar mijinta

Rahoton ya bayyana cewa mazan sunyi layi a kofar dakin otel din, inda suke shiga daya bayan daya suna yin lalata da ita.

Gidan talabijin na Isra'ila ya ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka yi mata fyaden ya shiga dakin a matsayin ma'aikacin lafiya, amma sai yayi amfani da wannan damar shima yayi mata fyade.

Yanzu haka dai hukumomi na jiran fitowar sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata, inda mutum biyu da ake zargi suke da hannu masu shekaru 27.

Da yake magana akan wannan fyade a shafinsa na Twitter, firaministan kasar Benjamin, Netanyahu, ya ce: '"Wannan abin firgitarwa ne, babu wata kalma da zan iya karawa".

"Wannan ba wai iya laifi bane akan yarinyar kawai, laifi ne akan al'ummar duniya baki daya da ya kamata ayi Allah wadai dashi sannan kuma a dauki mataki akan wadanda ke da hannu a ciki," cewar Netanyahu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel