Tsarkaketa nake yi - Faston da ake zargi da yi wa yarinya fyade

Tsarkaketa nake yi - Faston da ake zargi da yi wa yarinya fyade

Wani babban fasto mai shekaru 57, mai suna Ebenezer Ogunmefun, ya shiga hannun 'yan sanda kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke zama a Abeokuta.

Ana zargin babban faston da yi wa yarinya mai shekaru 15 fyade, wacce mahaifiyarta ta kai ta cocin don tsarkakewa.

A yayin da aka gurfanar da faston a kan zargin cin zarafi, dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Moshood Hammed, ya sanar da kotun cewa faston yana zama ne garin Abeokuta.

Faston na zama a gida mai lamba daya, titin Farfesa Ajibo Toluca a yankin Olomore da ke Abeokuta a jihar.

Ya sanar da cewa mahaifiyar yarinyar da kanta ta mika ta ga faston domin 'tsarkakewa' daga miyagun aljanu.

Faston ya sa yarinyar ta yi rantsuwa da bibul cewa ba zata sanar da kowa cewa ya yi mata fyade ba yayin da yake raba ta da miyagun aljannun.

Dan sanda mai gabatar da kara, ya ce laifin ya ci karo da sashi na 33 na dokokin hakkin kananan yara na jihar Ogun na 2006.

Duk da faston ya musanta aikata laifin, alkalin ya bada belinsa daga bisani, tare da dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Satumban 2020.

Mai shari'a Solomon Banwo, ya bada belin faston a kan kudin N750,000 tare da tsayyayyu biyu. Mai shari'ar ya ce daga cikin tsayayyun, daya dole ta zama matarsa, yayin da dayan zai zama shugaba a yankin.

Tsarkaketa nake yi - Faston da aka kama yana yi wa yarinya fyade

Tsarkaketa nake yi - Faston da aka kama yana yi wa yarinya fyade. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata

A wani labari na daban, wata kotun Majistare da ke zama a Ikeja a ranar Laraba, ta bada umarnin tsare wani saurayi mai shekaru 37 a gidan gyaran hali da ke Kirikiri a jihar Legas.

Saurayin mai suna Abdulmalik, ana zarginsa ne da cin zarafin karamar yarinya mai shekaru hudu a duniya, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Alkalin kotun, Peter Nwaka, ya bai wa 'yan sandan umarnin mika takardun shari'ar gaban ofishin gurfanarwa na jihar Legas don shawara tunda bai saurari rokon da Malik ke yi ba.

Nwaka ya dage sauraron karar har zuwa ranar 29 ga watan Satumban 2020 don ci gaba. Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, ASP Benson Emuerhi, ya zargi Malik da aikata laifin a ranar 26 ga watan Fabrairu a gidansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel