Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki

Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki

Wani dan kasuwa, Abdullateef Babatunde, ya sanar da kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun a Ibadan cewa ta raba aurensa da matarsa, Omotayo, saboda ta tilasta ma sa karbar dan da ba nasa ba.

Abdullateef ya sanar da kotun hakane yayin da ya ke kare kansa a gaban alkalin kotun, Cif Henry Agabaje, bayan matarsa ta yi ikirarin cewa shi mugun mutum ne, a saboda haka a raba aurensu.

"Omotayo ta kasance mai cin amanar aure, na sha kamata tana aikata zina da maza daban-daban.

"Na kai kararta wurin iyayenta kuma sun bani tabbacin cewa za su yi mata magana domin ta sauya halinta.

"Amma maimakon ta sauya halinta, Omtayo sai ta kara fandarewa, ta koma karuwanci da gaske, lamarin da ya tilasta min kaurace ma ta tunda ta dauki wata hanya ta daban.

"Ta na da yaro tare da daya daga cikin masoyanta. Na taba kamata da kato a shago.

"Sau biyu saurayinta ya na dirka ma ta ciki. Mata ta malalaciya ce kuma marar tarbiyya,'' a cewarsa.

Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki
Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki
Asali: Twitter

Da take kare kanta, Omotayo; mai sana'ar sayar da abinci, ta bayyana cewa mijinta ba son gaskiya ya ke yi mata ba saboda ya sha bata kudi ta je asibiti domin a zubar da juna biyunsu, yana mai fakewa da cewa bai shirya haihuwa ba.

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da ya sa kasashen duniya su ka daina sayarwa da Najeriya makamai

"Ya taba gudu ya barni na tsawon shekara biyu da rabi bayan na haifar ma sa yaron farko, sai daga baya ya dawo ya na rokona na yafe ma sa.

"Daga baya kuma ya zo ya fara korafin cewa ina sayar da abinci da daddare, shi ba ya so, duk da ba ya iya kulawa da ni da yaron da mu ka haifa," a cewarta.

Bayan iyayen ma'auratan sun amince da bukatar saki, alkalin kotun ya raba auren domin kowa ya samu zaman lafiya.

Alkalin kotun ya umarci matar ta cigaba da rike yaron da su ka haifa yayin da ya umarci Abdullateef ya ke biyanta alawus din N5,000 duk wata domin kulawa da yaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel