Babu dadewa harin 'yan bindigar daji zai yi kaura a Katsina - Sanata Barkiya

Babu dadewa harin 'yan bindigar daji zai yi kaura a Katsina - Sanata Barkiya

Sanata Kabir Barkiya, sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta tsakiya, ya bayyana cewa nan babu dadewa za a nemi 'yan bindigar daji da suka addabi jihar Katsina a rasa.

Barkiya ya sanar da hakan ne a yayin da yake jawabi ga manema labarai a majalisar dattawa a Abuja a ranar Alhamis.

"Babu shakka 'yan daban daji sun gigita jihar Katsina. Amma kokarin da dakarun sojin Najeriya da 'yan sanda wurin kawo karshen 'yan bindigan a ciki da wajen jihar suke yi abin godiya ne. Babu dadewa za a nemi masu laifin a rasa.

"Masu ruwa da tsaki a jihar Katsina sun hada kai wurin ganin karshen 'yan bindigar daji, wanda babu shakka zai zo karshe," yace.

Babu dadewa harin 'yan bindigar daji zai yi kaura a Katsina - Sanata Barkiya
Babu dadewa harin 'yan bindigar daji zai yi kaura a Katsina - Sanata Barkiya. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

A wani labari na daban, El-Rufai, wanda ya zanta da shugaban cocin Anglika ta Najeriya, Rabaren Henry Ndukuba, wanda ya shugabanci wakilai wurin ziyartar gwamnan a gidan gwamnatin, ya ce "manyan masu assasa rikici sune wasu malamai da ke amfani da damar da suka samu wurin hada fitina a maimakon addini. Suna raba kan al'umma tare da assasa rikici."

Tun farko, Babban Rabaren Ndukuba ya ce "Na yarda cewa idan kiristoci da Musulmi za su tsaya a kan koyarwar addinansu, ba za su taba tada fitina ba kuma kasar nan za ta ci gaba."

Kungiyar manyan malaman addinin kirista na arewa, ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta bai wa yankin kudancin Kaduna tsaron da ya dace.

Shugaban kungiyar, JohnPraise Daniel, ya sanar da manema labarai hakan a garin Abuja a ranar Talata.

Ya ce dole ne a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kudancin Kaduna da gaggawa. Daniel, wanda shine ya kirkiro cocin Dominion ta duniya, ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da an damke wadanda ke aika-aikar da kuma masu daukar nauyinsu.

Ba tun yanzu, 'yan daban daji sun addabi yankin arewa maso yamma. Al'amuransu sun mamaye jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da sauransu.

Su kan shiga gari ko kauye inda suke kashe jama'a tare da awon gaba da shanunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel