Yadda batagari su ka yi wa wasu kananan 'yammata biyu fyade a gaban mahaifinsu - Rundunar 'yan sanda

Yadda batagari su ka yi wa wasu kananan 'yammata biyu fyade a gaban mahaifinsu - Rundunar 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Delta ta kama wasu batagari da su ka yi wasu 'yammata biyu; mai shekaru 14 da mai shekaru 16, fyade a gaban mahaifinsu a garin Ughelli da ke yankin karamar hukumar Ughelli ta Arewa.

Batagarin sun aikata hakan ne ranar Laraba yayin da suka shiga gidan mutumin domin aikata sata.

Jaridar Punch ta rawaito cewa batagarin matasan su hudu sun yi fashi a gidan tare da aikata fyade ga 'yammata biyu bayan sun ci abinci, sun sha giya, sun cika cikinsu, a gidan.

Wani dan kungiyar agaji ta sa kai, wanda ya nemi a boye sunansa, ya sanar da Punch cewa; "matasa hudu ne suka shiga gidan tare da aikata fyade ga kananan 'yammata biyu a kan idon mahaifinsu, sannan su ka saci N280,000 a gidan.

"Btagarin matasan su na dauke da muggan makamai da bindigu. Tagar gidan su ka karya, su ka shiga gidan su ka sace wayoyi takwas mallakar mazauna gidan.

"Sun saci N280,000 a gidan, sannan sun yi wa kananan 'yammata biyu fyade a gaban mahaifinsu.

"Daga cikin 'yammatan ne daya ta gane mutum guda, daga cikin 'yan fashin, mai suna Isaac Friday, wanda mazaunin yankin ne.

Da ya ke tabbatar da labarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, Onome Onovwakpyeya, ya ce har yanzu ana neman sauran batagarin sakamakon layar zana da su ka mata bayan samun labarin an kama abokinsu.

"Mun kama daya daga cikinsu. Mu na kokarin ganin mun cimma sauran ukun domin kamasu, amma a halin yanzu dai sun gudu," a cewar kakakin.

Yadda batagari su ka yi wa wasu kananan 'yammata biyu fyade a gaban mahaifinsu - Rundunar 'yan sanda

Jami'an rundunar 'yan sanda
Source: UGC

A wani labari da Legit.ng ta wallafa, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da cewa ta kashe wasu 'yan bindiga guda biyu tare da kubutar da mutane biyu da su ka sace a yankin karamar hukumar Dutsinma.

DUBA WANNAN: Abinda ya sa na ke rokon 'yan sanda su kasheni: Bidiyon dan fashi

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne yayin da jami'an rundunar 'yan sanda a karkashin atisayen 'Puff Adder' su ka dira yankin bayan samun rahoton bullar 'yan bindiga dauke da bindigu.

A cewarsa, rundunar 'yan sanda ta samu labarin cewa 'yan bindiga dauke da bindigu samfurin AK 47 sun shiga kauyen Kwaro da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a ranar 12 ga watan Agusta.

SP Isha ya kara da cewa 'yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Mohammed Auwal tare da sace wasu mutane biyu da dabbobi ma su yawa.

Kakakin ya bayyana cewa an yi musayar wuta a tsakanin 'yan bindigar da kuma jami'an rundunar 'yan sanda da su ka bi sahunsu a lokacin da su ke kokarin tserewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel