Turmi da tabarya: 'Yan sa kai sun kama matashi yana yi wa yarinya fyade

Turmi da tabarya: 'Yan sa kai sun kama matashi yana yi wa yarinya fyade

- Kungiyar 'yan sa kai a ranar Alhamis a jihar Ribas sun damke wani matashi mai shekaru 20 yana yi wa yarinya mai shekaru 16 fyade

- 'Yan sa kan sun kama matashin ne a kan yarinyar a cikin kango bayan samun kiran mazauna yankin na gaggawa

- A halin yanzu matashin yana hannun 'yan sanda kuma za a mika lamarin gaban sashen bincike na musamman

Kungiyar 'yan sa kai ta Diobu a ranar Alhamis, ta damke wani matashi mai shekaru 20 mai suna Uche yayin da yake yi wa yarinya mai shekaru 16 fyade a wani kango da ke titin Ekwe, Mile 3 Diobu, Fatakwal, jihar Ribas.

An gano cewa an kama mutumin a yayin da yake kan yarinyar wurin karfe 1 na rana. Mazauna yankin ne suka kama shi tare da abokansa yayin da suka ja matashiyar budurwar cikin ginin.

Kamar yadda yace, shugaban kungiyar 'yan sa kan, Godstime Ihunwo, an kama wanda ake zargi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

Ihunwo ya sanar da Punch Metro cewa jami'ansa sun gaggauta zuwa bayan rahoton da suka samu daga mazauna yankin.

Ya kara da cewa, yayin da aka mika wanda ake zargin hannun 'yan sanda, abokansa sun tsere.

Turmi da tabarya: 'Yan sa kai sun kama matashi yana yi wa yarinya fyade

Turmi da tabarya: 'Yan sa kai sun kama matashi yana yi wa yarinya fyade. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

Ya ce, "Wurin karfe 1 na rana, wasu sun kira daga titin Ekwe, Mile 3 Diobu, Fatakwal, cewa sun ga wasu matasa suna kokarin yi wa yarinya fyade. Da gaggawa na tura jami'ai wurin.

"A lokacin da suka isa wurin, sun kama Uche yana yi wa yarinyar mai shekaru 16 fyade. Sun damke sa tare da kawo shi ofishin mu.

"Na kira shugaban hedkwatar 'yan sandan yankin wanda ya turo jami'ansa suka tafi da shi.

"Su uku ne suke aikata lamarin amma sauran sun tsere. Uche kadai aka kama yayin da yake kan yarinyar."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya tabbatar da cewa kwamishinan 'yan sanda, Joseph Mukan, ya umarci a mika lamarin gaban sashen bincike na musamman.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel