Yanzu-yanzu: Diyar Buhari, Hanan, za ta auri hadimin minista Fashola

Yanzu-yanzu: Diyar Buhari, Hanan, za ta auri hadimin minista Fashola

Hanan, daya daga cikin'yayan shugaba Muhammadu Buhari zata auri Muhammad Turad, babban mai baiwa tsohon gwamnan Legas kuma Ministan ayyuka na yanzu, Babatunde Raji Fashola, shawara.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa za a yi daurin auren ne ranar 4 ga Satumba, 2020.

Muhammad Turad 'da ne ga wani tsohon dan majalisan wakilai, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban, wanda ya wakilci mazabar Zariya tsakanin Mayun 2003 da 2007.

Hakazalika mahaifinsa ya yi takaran kujeran gwamnan Kaduna karkashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria, ACN.

Hanan ta karanci ilimin hoto a Jami’ar Ravensbourne dake Ingila.

Yanzu-yanzu: Diyar Buhari, Hanan, za ta auri hadimin minista Fashola
Yanzu-yanzu: Diyar Buhari, Hanan, za ta auri hadimin minista Fashola
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel