Alkali ya daure mutumin da aka kama da laifin yin lalata a Jihar Ogun

Alkali ya daure mutumin da aka kama da laifin yin lalata a Jihar Ogun

A jiya Laraba ne wani babban kotu da ke garin Abeokuta a jihar Ogun, ya yankewa Ugochukwu Obiakor hukuncin daurin shekaru 25 a gidan maza.

Mista Ugochukwu Obiakor zai yi zaman kaso na tsawon shekara 25 ne bayan Alkali ya same shi da laifin yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekara 11 fyade.

Bayan tsawon lokaci ana bincike, Alkali mai shari’a Mosunmola Dipeolu ya kama Ugochukwu Obiakor da laifin tarawa da karfin tsiya da wannan karamar yarinya.

Mista Obiakor ya yi ikirarin cewa bai aikata wannan laifi na fyade da ake tuhumarsa da shi ba.

A karshe kotu ta kama wannan mutumi mai shekaru 36 da haihuwa da laifi bayan la’akari da tarin hujjojin da aka gabatar a gaban babban kotun na jihar Ogun.

Bayan hujjoji sun gaskata zargin aikata fyade da ake yi wa wannan mutumi, Alkali Mosunmola Dipeolu ya ce Obiakor zai yi zaman kaso tare da mummunar ukuba.

KU KARANA: Fyade ya jawo an yankewa tsoho hukuncin kisa

Lauyan wanda ya ke kara, James Mafe, ya shaidawa kuliya cewa Ugochukwu Obiakor ya aikata wannan laifi ne a kauyen Omu-Aleku a ranar 4 ga watan Satumba, 2017.

Wannan lauya ya ce sakamakon gwajin da aka yi a asibiti ya nuna cewa an barka yadin wannan karamar yarinya a sanadiyyar saduwa da aka yi da ita da karfi da yaji.

Yadda abin kuwa ya faru shi ne Obiakor ya zo shagon mahaifiyar wannan yarinya ne ya yi cefane, can daga baya sai ya dawo shagon bayan tsohuwar ta fita, ya iske ta.

Daga nan ne Obiakor ya fadawa yarinyar ta bi shi gida domin ta karbo wasu kudi da ake bin sa bashi a shagon. A haka ya kai ta cikin wani kango, ya yi lalata da ita.

Obiakor ya aikata wannan ta’adi ne a gefen shagon mahaifiyar yarinyar a garin Mowe, Ogun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel