Da dumi-dumi: An sauke shugaban jami'ar Legas

Da dumi-dumi: An sauke shugaban jami'ar Legas

Hukumar Jami'ar Legas a ranar Laraba ta sanar da korar shugaban jami'ar, Farfesa Olawatoyin Ogundipe.

An sanar da korar ne yayin taron mahukunta jami'ar ta UNILAG da aka gudanar a Hukumar Kula da Jami'o'i na Kasa da ke Abuja.

Yayin da mutum bakwai suka jefa kuri'ar amincewa da tsige Ogundipe, mutum huɗu ba su amince ba; ɗaya daga cikinsu ya ce kamata ya yi a dakatar da shi.

Yanzu-yanzu: An sauke shugaban jami'ar Legas
Yanzu-yanzu: An sauke shugaban jami'ar Legas
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

Shugaban Jami'ar ta UNILAG, kuma shugaban majalisar jami'ar, Dr Wale Babalakin ne ya jagoranci taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164