Yanzu: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas da hafsoshin tsaro
Rahotannin da muke samu na nuni da cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya shiga ganawa da gwamnoni shida na jihohin Arewa maso Gabas.
A cewar wakilin gidan talabijin Channels TV, gaba daya hafsoshin tsaro tare da sifeta janar na rundunar 'yan sanda na cikin mahalarta taron.
Taron na gudana ne bayan da gwamnonin a makon da ya wuce suka zabi gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar.
KARANTA WANNAN: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki

Asali: Facebook
Gwamnonin sun sha alwashin yin hadaka don kawo karshen Boko Haram, sun kuma bukaci gwamnati ta karawa rundunar tsaro makamai da kayan yaki.
Cikakken labarin yanzu zuwa...
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng