Obaseki ya aikata laifin da ya cancani a tsigeshi - Tinubu ya yi tsokaci

Obaseki ya aikata laifin da ya cancani a tsigeshi - Tinubu ya yi tsokaci

Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanya albarkacin bakinsa cikin dambarwan siyasan dake gudana a majalisar dokokin jihar Edo.

Tinubu ya daura laifin dukkan abubuwan dake faruwa kan gwamna jihar, Godwin Obaseki, inda ya ce an ci mutuncin demokradiyya.

A jawabin da ya saki daren jiya, Tinubu ya ce tare kofar majalisa domin hana yan majalisa shiga a rantsar da su cin mutunci ne ga kundin tsarin mulki.

Ya bayyana cewa "Abubuwan da Gwamna Obaseki yayi a shekara daya da ya shude ko shakka babu ya cancanci a tsigeshi"

Ya kara da cewa duk da haka "wadannan yan majalisan basu yi barazanar tsigeshi ba. Kawai manufarsu ita ce su gudanar da ayyukansu kamar yadda al'ummarsu suka bukacesu."

A cewarshi, "Dalilin hana zababbun yan majalisan dokokin jihar Edo aikinsu da doka ta bukacesu, gwamna Obaseki ya yaudari al'ummar jiharsa kuma ya bayyana jahilcinsa ga kundin tsarin mulkin Najeriya a fili."

Ya ce a matsayin gwamna, ya kamata a ce Obaseki "ya sani fiye da gamarin mutane kafin hana majalisa dokokin jihar amma yana bukatan a koya masa darasi yanzu."

Obaseki ya aikata laifin da ya cancani a tsigeshi - Tinubu ya yi tsokaci
Obaseki ya aikata laifin da ya cancani a tsigeshi - Tinubu ya yi tsokaci
Asali: UGC

KU KARANTA: Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona

A bangare guda, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya mayarwa gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje martani mai zafi don ya ce babu aikin a zo a ganin da yayiwa al'ummar Edo.

Yayinda yake magana a fadar shugaban kasa ranar Juma'a, Ganduje wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo ya ce gazawar Obaseki zai saukaka musu wajen samun nasara a zaben ranar 19 ga Satumba.

Amma martani kan jawabin Ganduje, mai magana da yawun Obaseki, Crusoe Osagie , ya ce Ganduje bai da alhakin auna kokarin Obaseki saboda "irin bidiyon da ya bayyana kansa yana cusa Dalan da ya karba daga yan kwangila."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel