Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya daga hannun Ize-Iyamu
Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ya daga hannun kuma ya bada tuta wa dan takaran kujeran gwamnan Edo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) , Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Shugaba Muhammadu Buhari yayi hakan yayin Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ne ya kawo Ize-Iyamu fadar shugaban kasa, Daily Trust ta samu rahoto.
Daga cikin tawagar akwai shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna jihar Edo kuma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Abubuakar taiku Bagudu.
Da yiwuwan jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta gobe a Benin.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng