Bayan dukana, tsirara yake min a titi - Matar aure mai bukatar saki

Bayan dukana, tsirara yake min a titi - Matar aure mai bukatar saki

Wata malamar makaranta mai suna Iyabo Amusan a ranar Alhamis, ta garzaya gaban wata kotun gwargajiya da ke Mapo inda ta bukaci alkali da ya raba ta da mijinta saboda tsananin fushinsa.

Kamar yadda Iyabo ta sanar, ta ce ta amince da barin 'ya'yan a hannun Joseph amma in har za ta rabu da shi tare da samun kariya a rayuwarta.

"Joseph ya saba bata min suna tare da kirana macuciya.

"Mai shari'a, ban san me yasa Joseph ya yanke hukuncin tozarta ni da ci min mutunci ba. A kowacce rana, rigima ta daban ce a gida na.

"Duk lokacin da ya dukeni, yana min tsirara. Yana zargina da mallakar kwalin bogi wanda na samu aiki da shi.

"Mummunan kudirin Joseph a kaina shine ganin bayana. Ya taba sassara ni da adda inda nayi doguwar jinya a asibiti.

"Duk da haka, baya bani abinci tare da 'ya'yana. Ina biyan haya da kaina," Iyabo tace.

Joseph, madakin mace, ya amince da bukatar sakin amma ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Bayan dukana, tsirara yake min a titi - Matar aure mai bukatar saki

Bayan dukana, tsirara yake min a titi - Matar aure mai bukatar saki. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata

"Mai shari'a, ni ba manomi bane kuma babu wata bukata ta amfani da adda.

"Iyabo ta saba guduwa daga gida na inda daga bisani take bayyana a lokacin da ta so.

"Iyabo tana siyo kayayyakin amfanin gida tare da jan kunnena a kan kada in taba kuma ina kokarin kiyayewa.

"Ina bada N20,000 a matsayin gudumawata ta kudin haya," Joseph yace.

A yayin bada shaida, dan uwan Joseph ya tabbatar da cewa Iyabo muguwar mata ce mai bakin hali. Ta saba bao wa mijinta kunya a gaban jama'a inda ta kan jefe shi da zargin sata.

A jawabinta, diyarsu na farko, wacce take gidan aure zata iya bada shaida a kan mahaifinta.

Kotun ta kira diyar a wayar tafi da gidanka inda ta tabbatar da cewa mahaifinta babban dan wulakanci ne kuma abun kunya ne a gareta ta kira shi da mahaifi.

Alkali Ademola Odunade, shugaban kotun, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Satumba don yanke hukunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel