DSS sun kama matasan da su ka fara zanga - zangar juyin hali a kudancin Najeriya

DSS sun kama matasan da su ka fara zanga - zangar juyin hali a kudancin Najeriya

Da safiyar yau, Laraba, ne jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka kama Olawale Bakare da wasu sauran mutane shida da ke sanye da huluna ruwan dorawa a yayin da su ka fito gudanar da zanga-zangar juyin juya hali.

Jami'an DSS sun kama matasan ne a yankin Olaiya da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Matasan a karkashin jagorancin Bakare sun yi tattaki zuwa ofishin 'yan jarida domin gabatar da jawabi a kan zanga-zangar da su ka fara.

A yayin da matasan su ke jira a gaban ofishin 'yan jaridar domin a yi mu su iso, sai wasu 'yan sanda su ka tunkarosu tare da fara tattaunawa dasu.

A yayin da su ke tattaunawa ne sai ga wasu jami'an tsaron na hukumar DSS sun dira a wurin tare da yin awon gaba da matasan.

DSS sun kama matasan da su ka fara zanga - zangar juyin hali a kudancin Najeriya
'Yan sanda yayin kokarin tarwatsa ma su zanga - zangar juyin hali
Asali: Facebook

Kazalika, jami'an rundunar 'yan sanda sun tarwatsa matasan da su ka fito zanga-zangar juyin juya hali da safiyar ranar Laraba a yankin Ikeja.

Jami'an rundunar 'yan sanda sun katse zanga - zangar da matasan su ka fara da misalin karfe 10:00 na safe.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa

'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa matasan.

Sai dai, wasu daga cikin matasan sun tirje, inda suka kwanta a kasa tare da rike takardun da su ke dauke dasu.

Hakan ya tilasta jami'an tsaro yin harbin iska domin tarwatsa ma su zanga-zangar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami'an 'yan sanda sun kama matasa 60 daga cikin matasan da su ka fito zanga-zangar juyin juya hali a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel