Masu fyade 27 sun shiga hannun ‘yan sanda a jihar Bauchi

Masu fyade 27 sun shiga hannun ‘yan sanda a jihar Bauchi

- Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta damke wasu da ake zargi da aikata miyagun ayyuka a jihar

- Daga cikin wadanda aka kama harda wasu 27 da ake zargi da aikata fyade

- Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Wakili ya ce ana kan gudanar da bincike a kan lamuran na fyade da kungiyar asiri a jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, sun kama wasu mutum 27 da ake zargin masu fyade ne, da kuma wasu ‘yan kungiyar asiri su biyar da ke da nasaba da aikata miyagun ayyuka, tayar da zaune tsaye da kuma mallakar makamai.

A cikin wata sanarwa, jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Ahmed Mohammed Wakili, ya ce: “A ranar 17 ga watan Yuli 2020, wani Mallam Usman Muhammad ya kai kara ofishin yan sandan Dewu, cewa ya ga wani Abubakar Muhammed mai shekaru 25 na kauyen Riban Garmu da ke karamar hukumar Kirfi da yaran wani Dahiru Aliyu mata su biyu, a bayan wani asibiti a kauyen Riban Garmu a cikin duhu kuma a yayinda ake ruwan sama."

Masu fyade 27 sun shiga hannun ‘yan sanda a jihar Bauchi

Masu fyade 27 sun shiga hannun ‘yan sanda a jihar Bauchi Hoto: Daily Trust
Source: Depositphotos

Ya ce wanda ake zargin ya kama yara matan su biyu ta karfi sannan ya rufe masu bakunansu inda ya yi masu fyade. Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno

Jawabin ya ci gaba kamar haka: “A ranar 28 ga watan Yuni 2020, wani Magaji Shehu na Ramin Kasa Azare ya kai kara ofishin yan sanda cewa ‘yarsa mai shekara 12 mai suna Fatima Yusuf na Ramin Kasa Azare, ta sanar da shi cewa lokuta da dama a cikin shekarar 2020, wani Ahmed Sulaiman mai shekara 35, da Nasiru Shuaibu na Tashar Gadau, Azare, da Sani Inua mai shekara 34 na Tsakuwa Azare, da wani Achichi, sun hadu sun yaudare ta sannan suka yi lalata da ita."

DSP Wakili ya ce ana kan gudanar da bincike a kan lamuran na fyade da kungiyar asiri a jihar.

A gefe guda, mun ji cewa hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Adamawa, ta samu nasarar cafke wani saurai dan shekara 18 da ake zargi da lalata wata 'yar karamar yarinya .

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel