'Yan sanda sun kama saurayin da ya yi wa 'yar shekara 2 fyade

'Yan sanda sun kama saurayin da ya yi wa 'yar shekara 2 fyade

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Adamawa, ta samu nasarar cafke wani saurai dan shekara 18 da ake zargi da zakkewa wata 'yar karamar yarinya mai shekaru biyu kacal a duniya.

Saurayin ya fito ne daga yankin Jambutu Aso Rock da ke karashin karamar hukumar Yola ta Arewa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, saurayin ya dauki yarinyar ne da zummar kasancewar makwabci na gari zuwa wata makarantar Firamare ta Bekaji inda ya keta mata haddi.

Daga bisani, mahaifiyar 'yar karamar yarinyar ta lura da alamun sauyi a tattare da diyarta, inda babu wata-wata ta ranakarya zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa.

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya; Muhammadu Adamu

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya; Muhammadu Adamu
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, shi ne ya bayar da tabbacin hakan a ranar Laraba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.

DSP Nguroje ya ce a yayin da ake ci gaba da bincike, a halin yanzu yarinyar tana gadon asibiti karkashin kulwar kwararru a fannin kiwon lafiya.

A wani rahoton daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, ana zargin wani mutum mai shekaru 47 mai suna Olabode Oluwaseun da laifin yi wa matarsa mai dauke da juna biyu dukan da ya kai ta lahira.

An gano cewa Olabode ya bigi matarsa mai suna Blessing ne a ciki wanda yasa ta mutu tare da cikin.

KARANTA KUMA: Abinda ya kamata ku sani game da layin dogo mai amfani da lantarki da Ganduje zai gina a Kano

An gurfanar da wanda ake zargin a kan laifi daya a gaban wata kotun majistare, sakamakon laifin da ake zargin ya aikata a ranar 3 ga watan Afirilu a gida mai lamba 56, yankin Oke-Agba da ke Akure.

An zargesa da dukan matarsa ta bangaren dama a cikinta wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta da dan dake cikinta.

'Dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Uloh Goodluck, ya sanar da kotun cewa laifin abin hukuntawa ne a karkashin sashe na 319, sakin layi na 1 na dokokin laifuka na jihar Ondo.

Uloh ya ce, wannan shari'a ce ta kira kuma ya bukaci kotun da ta bada umarnin tsare Olabode a hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da za su samu shawara daga sashen gurfanarwa na jihar.

Lauyan Olabode, A. Ololike, bai soki bukatar adana wanda ake zargin ba a hannun 'yan sanda.

Alkali mai shari'a, N. T Aladejana, ya bada umarnin ci gaba da tsare Olabode a hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da za su samu shawara daga DPP.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel