Bidiyo: Karuwa ta tsallake ta taga bayan matar mai gida ta iso

Bidiyo: Karuwa ta tsallake ta taga bayan matar mai gida ta iso

- Wani bidiyo da ke yaduwa a kafafen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce

- A bidiyon, an ga wata mata wacce ake zargin karuwa ce tana tsallake taga, bayan matar mai gida ta buga kofa

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, mai nadarsa kawar wacce ke tsallake tagar ce inda take ta yi mata dariya

Wani bidiyo da ke yawo kwanakin nan a kafafen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce, jaridar The Nation ta ruwaito.

A bidiyo, an ga wata wacce aka zargin karuwa ce tana tsallake taga don gujewa abinda zai iya kaiwa ya kawo.

An ganta tana ficewa daga gidan ta taga bayan matar saurayinta ta buga kofa da niyyar shiga gidan.

A bidiyon, an ga karuwar tana fita ta taga yayin da kawarta wacce ke waje ke dariya tana daukarta ta a waya.

KU KARANTA: Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel