An kori ministan Ilimin Zambia bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a gari

An kori ministan Ilimin Zambia bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a gari

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu a ranar Laraba ya kori ministan Iliminsa, David Mabumba a cewar fadar shugaban kasar bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a kafafen sada zumunta.

Sanarwar daga fadar shugaban kasar ba ta fayyace dalilin korar ministan ba amma hakan ne zuwa ne bayan an saki bidiyon tsiraicin ministan a Twitter, Facebook da kuma Whatsaapp.

Ta ce kawai Lungu "ya soke nadin da ya yi wa ministan ilimi ... nan take," kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An kori ministan Ilimin Zambia bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a gari

An kori ministan Ilimin Zambia bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a gari. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

An nada David Mabumba mai shekaru 49 a matsayin minista ne a gwamnatin Lungu a shekarar 2016.

A wani labarin, wata gyatuma mai shekaru 80 a yankin Phatthalung a kasar Thailand tana gida a kwance ana yi mata karin ruwa bayan wani mutum mai shekaru 50 da ya yi mata fyade a ranar 21 ga watan Yuli.

Wacce abin ya faru da ita ta shaidawa manema labarai cewa tana sayar da shinkafa ne a cikin ganyen ayaba sai wani mutum mai kimanin shekaru 50 ya iso inda ta ke.

Ta ce ya rika yi mata hira mai sanyaya zuciya inda ya ce ya dade yana kaunar ta tun lokacin tana da kuruciyya a yayin da suke makwabtaka.

Ya fada mata cewa zai siya dukkan shinkafar amma za ta bi shi zuwa gidan dan uwansa inda zai basu abincin.

Sun yi ciniki sun amince zai biya ta Bt2,000 (S$90).

A hanyar su na zuwa gidan yan uwan nasa sai ya canja hanya ya tsawa a wani kango, a cewar ta.

Nan take ne ta fahimci abinda ya ke niyyar aikatawa kuma ta yi kokarin tserewa amma ta kasa. Ta ce bayan ya gama yi mata fyade ya kuma sace karamin jakar ajiyar kudaden ta.

Yan uwan, a halin yanzu suna neman yan sanda su binciko mutumin su kama shi da gaggawa.

Yan sandan a ranar Talata sun ce sun fara tattara bidiyon da naurorin tsaro na CCTV suka dauka kuma sun fara yi wa mutanen unguwar tambayoyi da niyyar samun bayani da zai tamaka a kama mutumin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel