Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB

Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jarabawar kammala karatun sakandare da hukumar jarabar kasa NECO ke shiryawa zai fara ranar 5 ga Oktoba, 2020 kuma a kammala 18 ga Nuwamba, 2020.

Gwamnatin ta kara da cewa hukumar jarabawar NABTEB za ta kaddamar da nata jarabawan ranar 21 ga Satumba kuma a kammala 15 ga Oktoban, 2020.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba, ya sanar da ranakun jarabawan ne a karshen tattaunawar kwana biyu da yayi da shugabannin hukumomin jarabawar na kasa.

A takardar da kakakin ma'aitakar ilimi, Ben Goong, ya saki, ya ce ma'aikatar ta ce za'a a iya fara jarabawar shiga makarantun sakandaren gwamnatin tarayya ranar 17 ga Oktoba, 2020.

Bugu da kari, jarabawar BECE da daliban aji uku a makarantun sakandare da NECO ke shiryawa zai fara ranar 24 ga Agusta kuma a kammala 7 ga Satumba, 2020.

Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB
Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB
Asali: Depositphotos

Asali: Legit.ng

Online view pixel