Uba ya samu daurin shekaru 20 a kurkuku saboda lalata ‘Yar sa mai shekara 12

Uba ya samu daurin shekaru 20 a kurkuku saboda lalata ‘Yar sa mai shekara 12

Wani kotu na musamman a Legas da ke sauraron karar fyade da rigimar iyali ya yankewa wani ‘dan acaba mai shekaru 37 daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.

Jaridar Vanguard ta ce wannan kotu da ke zama a garin Ikeja ya samu Emmanuel Idoko da laifin keta alfarmar ‘diyar cikinsa mai shekara 12 da haihuwa.

Alkali Sybil Nwaka yayin da ya ke zartar da hukunci ya ce masu kara sun gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Mista Emmanuel Idoko ya aikata wannan laifi.

An daure Emmanuel Idoko ne bisa laifin cusa hannunsa a cikin al’aurar wannan Baiwar Allah.

Alkalin ya ce: “An samu wanda ake kara da laifin lalata ta hanyar tarawa ba tare da izni ba, wanda hakan ya sabawa sashe na 261 na dokokin laifin jihar Legas na shekarar 2015.”

“Don haka an yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.”

Babajide Boye wanda shi ne Lauyan da ya tsayawa yarinyar da aka boye sunanta, ya bayyana cewa uban na ta ya aikata wannan laifi ne a gidansu da ke Oworoshoki, Legas a 2017.

KU KARANTA: Malamai ba su goyon bayan a rika yi wa masu fyade dandaka

Boye ya ce: “Ya yi lalata da karamar yarinyar cikinsa mai shekara 12 ta hanyar cusa yatsunsa a cikin al’aurarta."

Kamar yadda rahoton ya bayyana, da ake wannan shari’a, mutane hudu ne su ka bada shaida a kan Idoko, yayin da shi kadai ne ya bada shaida domin ya kare kansa.

A watan Maris, 2019, wani Likita mai suna Dr. Oyedeji Alagbe da ake aiki da cibiyar Mirabel Center da ke kula da larura irin wannan, ya bada shaida a gaban kotu.

Dr. Alagbe ya shaidawa Alkali mai shari’a cewa: “Wanda ta ke kara ta bada labari cewa mahaifinta bai auri mahaifiyarsu ba, amma ita da ‘yanuwanta su na zama a gidansa."

Yarinyar ta fara afkawa ta’adin mahaifinta ne tun 2016 lokacin da ya ji ana labarin cewa ta rasa budurcinta, don haka ya bukaci ya jarraba ya ganewa kansa halin da ta ke ciki.

“Ya ce zai yi amfani da mazakutarsa ya duba ko ta rasa budurcinta, sai ta ki yarda, ya yi mata duka, daga nan ya fara gallaza mata azaba a gida saboda ta ki yarda da rokonsa.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel