Kano: Majalisar malamai ta yi watsi da hukuncin dandage masu fyade

Kano: Majalisar malamai ta yi watsi da hukuncin dandage masu fyade

Majalisar malamai ta jihar Kano, ta yi watsi da bukatar majalisar jihar Kano na saka dokar dandake masu fyade, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan za mu tuna, a ranar 15 ga watan Yulin 2020, dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Rano, Nuraddeen Alhassan, ya mika bukatar kafa dokar dandake masu fyade a jihar.

A yayin martani a kan bukatar, shugaban majalisar malaman, Sheikh Ibrahim Khalil, ya kalubalanci bukatar tare da bukatar dokokin shari'a na 2000 su sake dubawa.

Khalil ya ce, matsayar majalisar ba tana bayyana cewa suna goyon bayan masu fyade ba ne.

Kamar yadda yace, majalisar malaman ta yanke hukuncin ziyartar majalisar jihar don bada shawara da kuma bayyana matsalar addinin Musulunci a kai.

Kano: Majalisar malamai ta yi watsi da hukuncin dandage masu fyade

Kano: Majalisar malamai ta yi watsi da hukuncin dandage masu fyade. Hoto daga Daily Nigerian
Source: UGC

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

A wani labari na daban, dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano, a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya maka gwamna Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya. A wannan karon, ba zargin magudin zabe bane, zargi ne na daban ya kai su gaban kotun.

Abba gida-gida ya shigar da kara ne mai kalubalantar matakin da Ganduje ya dauka na mallakawa wasu sanannun 'yan kasuwa, mamallakan kamfanonin Mudatex da El-Samad babban otal na Daula.

Ba nan kadai gwamnan ya tsaya ba, ya mallaka musu gagarumar tashar Shahuci da ke cikin birnin Dabo.

Lauyan Abba Kabir Yusuf, Barista Bashir Yusuf, ya bayyana cewa hakan ya yi karantsaye ga tsarin kundun tsarin mukin kasar nan da ya yi magana a kan hakkokin mallakar kasa ko filaye.

Amma kuma, daga bangaren gwamnatin jihar, ya ce ba su san da labarin shigar da wannan karar ba.

Hakazalika, lauyan Abba gida-gida ya sanar da kotun cewa akwai bashi don gina titin jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki da gwamnatin ta ke yunkurin ciyowa daga China.

Ya tabbatar da cewa karbo wannan bashin zai jefa jihar Kano acikin halin ragargajewar tattalin arziki.

Ammam kuma lauyan Ganduje wanda shine antoni janar, kuma kwamishinan sharia'a na jihar kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko alamu babu na kamshin gaskiya a wadannan labaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel