Allura ta tono garma: Matashi, Haruna Mohammed, ya yiwa kakarsa fyade

Allura ta tono garma: Matashi, Haruna Mohammed, ya yiwa kakarsa fyade

Jami'an hukumar yan sandan jihar Ondo sun gurfanar da wani matashin manoni, Haruma Mohammed, kan laifin yiwa kakarsa, Ibukun Akinlo, yar shekara 50 fyade.

An gurfanar da Haruna ne a wata kotun Majistare kan laifi daya na fyade, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ce ya aikata laifin ne ranar 8 ga watan Yulu, 2020 a hanyar Lalepa/Akinfosile a unguwar Igbotako na jihar Ondo.

Lauyan yan sanda, Sifeto Augustine Omhenimhen, ya ce laifin ya sabawa sashe 358 na dokokin jihar Ondo.

Insfekta Augustine Omhenimhen ya bukaci kotun ta garkame mutumin a kuruku zuwa lokacin da zai saurari umurni daga ofishin hukunce-hukunce.

Shugabar kotun majistaren, Rasheedat Yakubu, ya bada umurnin garkame Haruna a ofishin yan sandan CID.

Allura ta tono garma: Matashi, Haruna Mohammed, ya yiwa kakarsa fyade

Allura ta tono garma: Matashi, Haruna Mohammed, ya yiwa kakarsa fyade
Source: Twitter

A wani labarin daban, wata kotun daukaka kara da ke Legas, ta yi watsi da karar da Adegboyega Adenekan, wani shugaban makaranta da aka daure na shekaru 60 a gidan gyara halayya ya daukaka.

An dai yanke masa hukuncin ne kan laifin yi wa yarinya mai shekaru biyu fyade .

An gurfanar da Adenekan a ranar 29 ga watan Janairun 2018 a kan aikata wa yarinya karama 'yar makaranta fyade a jihar Legas.

Alkalin kotun, Sybil Nwaka ya zartar da hukunci a ranar 24 ga watan Oktoban 2019, inda ya yankewa dattijon mai shekaru 47 shekaru 60 a gidan gyaran hali.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Nwaka ya bayyana Adenekan a matsayin "mugu, mara tausayi kuma dabba wanda bai cancanci yawo a titin Legas ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel