Daurin shekaru 60 a kan fyade: Kotun daukaka kara ta jaddada hukunci a kan Adenekan

Daurin shekaru 60 a kan fyade: Kotun daukaka kara ta jaddada hukunci a kan Adenekan

Wata kotun daukaka kara da ke Legas, ta yi watsi da karar da Adegboyega Adenekan, wani shugaban makaranta da aka daure na shekaru 60 a gidan gyara halayya ya daukaka.

An dai yanke masa hukuncin ne kan laifin yi wa yarinya mai shekaru biyu fyade .

An gurfanar da Adenekan a ranar 29 ga watan Janairun 2018 a kan aikata wa yarinya karama 'yar makaranta fyade a jihar Legas.

Alkalin kotun, Sybil Nwaka ya zartar da hukunci a ranar 24 ga watan Oktoban 2019, inda ya yankewa dattijon mai shekaru 47 shekaru 60 a gidan gyaran hali.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Nwaka ya bayyana Adenekan a matsayin "mugu, mara tausayi kuma dabba wanda bai cancanci yawo a titin Legas ba."

Daurin shekaru 60 a kan fyade: Kotun daukaka kara ta jaddada hukunci a kan Adenekan

Daurin shekaru 60 a kan fyade: Kotun daukaka kara ta jaddada hukunci a kan Adenekan Hoto: Thisday
Source: UGC

Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin, Adenekan ya garzaya kotun daukaka kara da bukatar a soke hukuncin kotun kasa.

Amma kuma, a hukuncin da aka zartar a ranar Litinin, kotun daukaka karar ta yi watsi da karar da ya daukaka tare da jaddada hukuncin kotun ta kasa.

KU KARANTA KUMA: Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid

A wallafar da kotun tayi a shafinta na Twitter, ta ce: "Kotun daukaka karar ta yi watsi tare da jaddada hukunci a kan Adegboyega Adenekan na makarantar Chrisland a yau 27 ga watan Yulin 2020."

A wani labarin kuma, wata kotun majistare ta hudu da ke zama a Birnin Kebbi, ta bukaci a adana mata wani ma’aikacin banki mai suna Hussaini Sahabi a gidan gyara hali.

Ana zargin matashin mai shekaru 25 da yin luwadi da wani yaro mai shekaru 10, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda aka shigar da karar, an zargi matashin mai aiki da wani banki a jihar da lalata karamin yaron.

An gurfanar da ma’aikacin bankin a ranar 21 ga watan Yulin 2020.

Dan sanda mai gabatar da kara mai suna Muntari Mati, ya sanar da kotun cewa, wanda ake zargin mazaunin kwatas din Gwadangwaji ne da ke cikin Birnin Kebbi. Ya aikata laifin ne a gidansa.

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 284 na dokokin jihar.

Alkalin kotun, Aminu Diri, ya dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Augusta. Ya bukaci a adana masa wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel