Bidiyo: Yadda na samu ciki da budurcina duk da ban taba jima'i da kowa ba - Budurwa

Bidiyo: Yadda na samu ciki da budurcina duk da ban taba jima'i da kowa ba - Budurwa

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani na Florence Wathoni Anyansi, daya daga cikin masu shirin gidan BBNaija na wannan shekarar nan ya bai wa jama'a da yawa mamaki.

Budurwar ta bayyana yadda ta samu juna biyu duk da kuwa da budurcinta kuma bata taba lalata da kowa ba a lokacin da take shekaru 23.

A bidiyon da a halin yanzu ya karade kafafen sada zumuntar zamani, mahaifiyar yaro dayan ta bayyana cewa ta samu dan wani lokaci tare da saurayinta suna shafe-shafen juna.

Daga nan ne ya goga mazakutarsa a gabanta har ya fitar da maniyyi duk da kuwa bai shiga ko ina ba.

Wathoni ta ce bayan aukuwar lamarin ta daina ganin al'adarta amma bata dauka al'amarin da muhimmanci ba saboda ta san ba zai yuwu ta samu ciki ba bayan basu yi wani abun a zo a gani ba.

'Yar shekaru 29 a halin yanzu, ta bayyana cewa ta gano tana dauke da juna biyu ne bayan watanni biyar da aukuwar lamarin sakamakon gwaje-gwajen da tayi.

KU KARANTA: Korar Sanusi II daga Kano da tsaresa: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar

"Har a lokacin da budurcina. A wannan ranar da muka yi soyayya da saurayina, ban taba tsammanin zan ga ciki ba saboda babu wani babban abu da ya shiga tsakaninmu.

"Saurayin nawa babu abinda yafi so da ya wuce ganin gaban mace. Ni kuwa na bar shi ya goga min mazakutarsa a gabana har ya fitar da maniyyi. A haka na samu ciki," tace.

"Bayan watanni biyar, na gano ina dauke da juna biyu. A lokacin nake tambayar kaina ta yaya hakan ta faru?

"Na gano hakan ne a wata safiyar Lahadi bayan da na ziyarci wani mai siyar da magani. Ya bani abun gwajin ciki inda na tabbatar da cewa ciki gareni," ta kara da cewa.

Wathoni ta tuna yadda ta dinga fama da wahala wurin haihuwa saboda a budurwa take har lokacin.

A yayin martani ga wannan ikirarin, Folashade Olugbemi, wata likita wacce ta yi bayani a kai, ta ce hakan na iya faruwa a kimiyyance.

Ta bayyana cewa koda namiji bai sadu da mace ba, matukar ya zuba maniyyi a gabanta, akwai yuwuwar ya karasa ciki da kanshi.

"Hakan na iya faruwa. Kamar yadda tace, akwai yuwuwar cewa a wannan lokacin akwai kwai a cikin ta. A gaskiya maza basu bukatar maniyyi mai tarin yawa wurin yi wa mace ciki," Olugbemi tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel