Yiwa yar shekaru 6 fyade: Kotu ta yanke wa wani mutumi daurin rai-da-rai

Yiwa yar shekaru 6 fyade: Kotu ta yanke wa wani mutumi daurin rai-da-rai

- Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Ishau Gruma wanda aka kama da laifin yiwa yarin 'yar shekaru 6 fyade a jihar Ekiti

- Lauyan wanda ake karar, K.K Adeniyi ya roki mai shari'ar da ya sassauta hukuncinsa, a cewarsa hukuncin daurin rai-da-rai ya yi tsauri

- Kwamishinan shari'a na jihar ya bayyana jin dadinsa kan hukuncin da cewar hakan zai zama izina ga masu yiwa kananun yara fyade

Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke da zama a Ado-Ekiti a ranar Litinin ta yankewa Ishau Gruma hukuncin daurin rai-da-rai bayan kamashi da laifin yiwa 'yar shekara 6 fyade.

Wanda aka yiwa hukuncin, Ishau Gruma, ya aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Yuli 2019, a Erio-Ekiti, karanar hukumar Ekiti ta Yamma.

Mai shari'a A.A Adeleye na babbar kotun jihar ta 5 ne ya yanke hukuncin bayan samunsa da laifin yiwa yarinyar fyade, duk da cewa ya musanta zargin.

Tawagar jami'an da suka shigar da kara bisa jagorancin babban antoni na jihar kuma kwamishin shari'a, Olawale Fapohunda, ya gabatar da mutane biyu da suka bada hujja kan zargin.

Yayin da bangaren masu kare wanda ake kara suka kira wanda ake tuhumar a matsayin shaida kawai.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kashe lauya a Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa

Lauyan wanda ake karar, K.K Adeniyi ya roki mai shari'ar da ya sassauta hukuncinsa, a cewarsa hukuncin daurin rai-da-rai ya yi tsauri.

Yiwa yar shekaru 6 fyade: Kotu ta yanke wa wani mutumi daurin rai-da-rai

Yiwa yar shekaru 6 fyade: Kotu ta yanke wa wani mutumi daurin rai-da-rai
Source: Depositphotos

Mai shari'a Adeleye, a hukuncin da ya yanke kan shari'ar, ya ce bangaren masu karar sun gabatar da hujjoji kwarara akan wanda ake zargin, don haka ya yanke masa daurin rai-da-rai.

Da yake magana kan hukuncin, kwamishinan shari'a na jihar kuma babban antoni, Olawale Fapohunda, ya bayyana jin dadinsa kan hukuncin da cewar "hukunci mai sauki wanda zai zama izina ga masu yiwa kananun yara fyade."

Fapohunda ya ce tsarin jihar na ta baci kan duk wani cin zarafi akan mata da kananan yara zai ci gaba da gudana ta hanyar yin hukunci a kotu da kuma tsoratar da masu irin wannan laifi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel