Sanatan Kano ta Tsakiya zai fitar da matasan 'yan kwallo 5 zuwa kasashen ketare

Sanatan Kano ta Tsakiya zai fitar da matasan 'yan kwallo 5 zuwa kasashen ketare

Tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar shiyyar Kano ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, ya sha alwashin zai fidda wasu hazikan matasa 'yan kwallo biyar zuwa kasashen ketare.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito, tsohon gwamnan zai fidda matasan biyar da za a zakulo daga kungiyarsa ta Shekarau Babes zuwa kungiyoyin kwallon kafa na kasashen ketare.

Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a da ta gabata yayin zantawa da shugabannin kungiyarsa ta kwallon kafa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Rahoton hakan ya fito ne daga bakin Ahmadi Babandi Gama, kakakin jagororin kungiyar ta Shekarau Babes a wata sanarwa da aka rarraba wa manema labarai.

Mallam Ibrahim Shekarau ya kuma bayar da tabbacin cewa, kungiyar za ta shiga a fafata da ita a gasar rukuni na daya wato Nigeria National League NNL a kakar wasa ta 2021/2022.

Mallam Ibrahim Shekarau
Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: UGC

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya mika bukatar gyara dokokin masarautar Kano na 2019 gaban majalisar jihar.

Kakakin majalisar jihar Kano, Abdul'aziz Gafasa, ya sanar da hakan ne a ranar Laraba da ta gabata a gaban majalisar.

Ana tsammanin 'yan majalisar zasu tattauna tare da yanke hukunci a kan bukatar kafin karshen watan Yulin 2020, jaridar Daiy Trust ta ruwaito.

Korarrun masu sarautar sun hada da Aminu Babba Dan Agundi wanda shine sarkin Dawaki Maituta da Sanusi Ado Bayero wanda shine Chiroman Kano.

Marigayi Ado Bayero ne ya kori Babban Dan-Agundi yayin da tubabben sarki Sanusi Lamido ya kori Sanusi Ado Bayero a kan zargin rashin biyayya.

Babba Dan Agundi ya kalubalanci tube masa rawani a kotu. Amma bayan shekaru 17 da aukuwar lamarin.

Kotun koli ta bai wa marigayi Ado Bayero gaskiya inda ta jaddada hukuncinsa.

KARANTA KUMA: Kwankwasiyya ta nemi kotu ta dakatar da Ganduje daga karbar rancen N300bn daga kasar China

Bayan da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya sake bukatar nada Babba Dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, Ganduje ya bukaci majalisar da ta gyara wasu dokokin masarautar na 2019 wanda suka hada da dokokin masu nadin sarauta.

A halin yanzu, Sanusi Ado Bayero ne Wamban Kano kuma dan majalisar nada sarakuna idan majalisar jihar ta amince da bukatar.

A 2003, marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya kori Babban Dan-Agundi a matsayinsa na hakimin Gabasawa kuma Sarkin Dawaki Maituta bayan zarginsa da yayi da rashin biyayya tare da kutsawa cikin al'amuran siyasa.

Korarren basaraken, Babba Dan-Agundi ya ki halartar gayyatar da aka yi masa gaban kwamitin da marigayi Ado Bayero ya kafa don bincike a kansa.

Babba Dan-Agundi ya kalubalanci tube masa rawani da aka yi a babbar kotun jihar inda kotun ta bada umarnin mayar da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel