Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade

Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Neja sun damke wani mutum mai shekaru 32 da laifin sata a gidan wata tsohuwa mai shekaru 60 tare da yi mata fyade.

Sani Garba, wanda ya aikata laifin a yankin Kuspa da ke karamar hukumar Suleja, ya shiga hannun 'yan sanda.

Tsohuwar mai shekaru 60 ta kai wa 'yan sanda rahoton sannan suka damke wanda ake zargin wanda mazauni ne kusa da yankin tsohuwar.

An kama wani mutum mai suna John Adamu mai shekaru 23 a kan zarginsa da ake da yi wa yarinya mai shekaru bakwai a Unguwan Nasarawa da ke karamar hukumar Kontagora ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan mai suna Abiodun Wasiu ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade

Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Korar Sanusi II daga Kano da tsaresa: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar sojin Operation WHIRL STROKE ta ceto mutu 34 da aka yi garkuwa da su, ta damke wasu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane tare da samo miyagun makamai a jihar Binuwai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a a garin Abuja.

Enenche ya ce, nasarorin da aka samu sun biyo bayan bayanan sirrin da suke samu ne a kan inda miyagun masu garkuwa da mutanen suke.

Sun dade suna addabar kauyen Igbom da ke gundumar Nenzev ta karamar hukumar Logo ta jihar Binuwai.

Kamar yadda yace, dakarun rundunar sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan wanda hakan ya kai ga kashe wani mutum daya mai suna Zwa Ikyegh, wanda bincike ya nuna shine shugaban kungiyar. Daga nan wasu daga cikinsu sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.

"Nasarar wannan arangamar ta sa an ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su wadanda suka shafe sama da wata daya a hannun miyagu.

"Dukkan wadanda aka ceto an mika su ga 'yan uwansu da ke karamar hukuamr Logo," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel