Yanzu-yanzu: Kwamishanoni 3 a gwamnatin Godwin Obaseki sun yi murabus, sun yi mubaya'a ga Ize-Iyamu (Jerinsu)
1 - tsawon mintuna
Kwamishanoni uku a hukumar cigabar yankuna masu arzikin mai da isakar gas na jihar Edo, sun yi murabus daga gwamnatin Godwin Obaseki, kuma sunyiwa abokin hamayyarsa, Osaze Ize-Iyamu, mubaya'a.
Rahoton TVC News ya bayyana cewa sun ajiye ayyukansu ne a yau Litnin, 27 ga watan Yuli, 2020.
Ga jerin sunayensu:
1) Hon Osamwonyi Atu
2) Hon Emmanuel Odigie,
3) Alhaji Rilwanu Oshiomhole
Asali: Legit.ng