Seyitan: Babu hujjar da ke nuna cewa D’Banj ya aikata fyade – ‘Yan Sanda

Seyitan: Babu hujjar da ke nuna cewa D’Banj ya aikata fyade – ‘Yan Sanda

- Wata Baiwar Allah Seyitan Babatayo ta na zargin D’Banj da yi mata fyade

- Wannan Mata ta kai kukan Tauraron gaban ‘Yan Sanda domin ayi bincike

- ‘Yan Sanda sun ce babu abin da ke gaskata zargin da ake yi wa Mawakin

Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun wanke shararren Mawakin nan wanda aka sani da D’Banj daga zargin da wata Seyitan Babatayo ta yi masa na yi mata fyade.

A wani jawabi da ‘yan sanda su ka fitar ta bakin DCP Umar Sanda a madadin mataimakin sufeta janar na kasa wanda ke lura da binciken laifuffuka, an yi fatali da wannan zargi.

Hukumar dilllacin labarai na kasa, NAN ta rahoto ofishin FCID na ‘yan sandan ya na cewa babu hujjar da ke nuna Tauraron ya yi lalata da Seyitan Babatayo da karfin tsiya.

“Gaskiyar lamarin shi ne a ranar 30 ga watan Disamba, 2018, Franklin Amudo wanda shi ne manajar wanda ta kawo kara, ya gayyaci Seyitan zuwa wani biki a otel din Eko Atlantic a Legas.”

KU KARANTA: COVID-19 ta sake harbin mutane 438 a Najeriya

Seyitan: Babu hujjar da ke nuna cewa D’Banj ya aikata fyade – ‘Yan Sanda

Seyitan da D'Banj
Source: Instagram

Miss Seyitan Babatayo ta jefi D’Banj da zargin yi ma ta fyade da kokarin yi wa maganar rufa-rufa.

Ko da cewa Seyitan ta yi wasa a wannan otel, jami’an ‘yan sanda sun ce babu abin da zai nuna Oladapo Daniel Oyebanjo ya yi lalata da ita, don haka aka kashe maganar.

Sanda ya ce bincike ya nuna babu gaskiya a korafin da Seyitan Babatayo ta yi na cewa Oladapo Daniel Oyebanjo watau D’Banj ya yi amfani da ita ba tare da iznin ta ba.

Jawabin na DIG ya kara da cewa: “An dakatar da wannan bincike a sakamakon babu hujjar da aka samu da ke nuna gaskiyar an yi wa wanda ta kawo kara fyade.”

Bayan haka wannan Budurwa ta karyata rade-radin da ake yi na cewa ta tuntubi Segun Awosanya da nufin janye korafin da ta ke yi a kan mawakin a gaban hukuma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel